Buhari ya kara wa'adin zangon kujerar alkalin alkalai Tanko Mohammed

Buhari ya kara wa'adin zangon kujerar alkalin alkalai Tanko Mohammed

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kara wa Tanko Mohammed wa'adin wata uku a kan kujerar alkalin alkalai na kasa da yake rikon kwarya.

A wani jawabi da ya fitar a ranar Asabar, kakakin hukumar kula da ma'aikatar shari'a (NJC), Soji Oye, ya ce shugaba Buhari ya aika takardar neman karin wa'adin ga hukumar a ranar Alhamis.

Shugaba Buhari ya fara nada Muhammad a matsayin alkalin alkalai na kasa a watan Janairu bayan dakatar da tsohon alkalin alkalai Walter, wanda ake zargi da kin bayyana dukkan kadarorin da ya mallaka.

A ranar Alhmis ne kotun da'ar ma'aikata ta tabbatar da samun Onnoghen da laifin da ake zarginsa da aikata wa na kin bayyana kadarorinsa da gangan, kotun ta haramta masa rike mukami na tsawon shekara 10.

Buhari ya kara wa'adin zangon kujerar alkalin alkalai Tanko Mohammed

Buhari da Tanko Mohammed
Source: UGC

Onnoghen ya musanta dukkan tuhumar da ake masa, kuma ya daukaka kara domin kalubalantar hukuncin da kotun ta yanke.

Dakatar da Onnoghen da Buhari ya yi ta jawo barkewar cece-kuce, wasu sun bayyana cewar matakin da shugaban kasar ya dauka ya saba wa kundin tsarin mulkin Najeriya.

DUBA WANNAN: Kisan fararen hula: Rundunar sojin sama ta mayar wa sarakunan Zamfara martani

Jawabin da NJC ta saki ranar Asabar ya musanta rahoton wata kafar yada labarai da ke nuna cewar hukumar za ta zauna cikin makon gobe domin tattauna kara wa Mohammed wa'adi a matsayin alkalin alkalai na rikon kwarya.

Ta bayyana cewsar tuni ta amince da bukatar yin karin wa'adi ga Mohammed.

"Sabanin rahotannin da wasu kafafen yada labarai ke yada wa a kan karin wa'adin kujerar riko ta alkalin alkalai, hukumar NJC ta amince da bukatar shugaba Buhari na yin karin wa'adin wata uku ga uku ga Jastis I. T. Muhammad tun ranar Alhamis," a cewar jawabin da NJC ta fitar ranar Asabar.

Sai dai, hukumar ta NJC ba ta fadi yaushe ne shugaba Buhari ya aika musu da bukatar neman yin karin wa'adin ga Jastis Mohammed ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel