Sarkin Kano ya ba da wasu dalilai da ya sa Najeriya ba za ta taba gyaruwa ba

Sarkin Kano ya ba da wasu dalilai da ya sa Najeriya ba za ta taba gyaruwa ba

- A wani taro da ya halarta a Abuja, Sarkin Kano Sanusi Lamido Sanusi, ya bayyana wasu dalilai da ya sa kasar Najeriya ba za ta taba cigaba ba

- Ya ce bala'in son mulki ne ya assasa rikcin kabilanci dana addini a fadin kasar nan

Sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sanusi na biyu, ya bayyana cewa kiran da ake yi na kawo gyara a kasar nan ba zai taba aiki ba, saboda manyan 'yan siyasar kasar nan suna amfani da wata dama da suke sake ruguza kasar nan saboda wata bukata ta su ta kansu.

Ya yi jawabin ne a jiya a gurin wani taro da aka gabatar a Abuja. Sarkin wanda ya aika da babban malami a fannin nazarin addinin Islama na Jami'ar Bayero da ke Kano, Dokta Bashir Aliyu Umar a matsayin wakilin shi, ya bayyana cewa ana amfani da kalmar gyara ne ana ruguza wasu muhimman abubuwa a kasar nan, sannan kuma ana kara kawo matsalar tsaro a kasar.

Sarkin Kano ya ba da wasu dalilai da ya sa Najeriya ba za ta taba gyaruwa ba
Sarkin Kano ya ba da wasu dalilai da ya sa Najeriya ba za ta taba gyaruwa ba
Source: UGC

"Bala'in son mulki da manyan 'yan siyasar kasar nan ke yi shi ne ya jefa mu cikin rikicin kabilanci dana addini a kasar nan, duk da dai cewa ana samun saukin rikicin a wasu wuraren, amma da ance an shawo kan wannan matsalar, sai kaji wani wuri kuma sun dauka.

"Muna da manya a kasar nan da suka amfana sosai da kayan gwamnati. Mutane iri na da wadanda suka girme ni, sun halarci makarantu tun daga firamare zuwa jami'a a makarantun gwamnati. Amma abin takaicin shine, maimakon su yi kokari su gyara irin wadannan makarantun domin cigaban wasu, sai suka koma sanya 'ya'yansu a makarantun kudi, wadda talaka ba zai iya kai na shi ba.

KU KARANTA: Jerin jihohin da suka shirya biyan albashin naira 30,000

"Hakazalika an bata bangaren kiwon lafiya, saboda yanzu mutane na zuwa kasar Indiya, Misra, da kasashen Turai domin neman magani. Wani lokacin ma kafin ku kai kasar da za ayi maganin sai rai ya yi halinsa," in ji shi.

A cewarsa, mutanen da suka karbi kasar a hannun sojoji sune suka assasa matsalar rashin tsaro, magudin zabe, cin hanci da rashawa, sannan sune suka bata ma'aikatar, hukumomin tsaro da sauran su. Ya ce abin takaici ne ace irin kasar da muke zaune cikinta kenan, bayan irin arzikin da Allah ya yi mana.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel