Buhari ya kwashi tsawon shekara 1 da kwana 39 a kasashen waje cikin shekara 3 da wata goma

Buhari ya kwashi tsawon shekara 1 da kwana 39 a kasashen waje cikin shekara 3 da wata goma

-Buhari ya ziyarce kasashe talatin da uku a wa'adinsa na farko

-Kasar Ingila itace wacce yafi zuwa yawanci saboda neman lafiya

A daidai lokacinda ya rage saura makonni kadan kafin wa’adin mulkinsa na farko ya kare, Shugaba Buhari ya kwashi tsawon kwanaki dari hudu da hudu wanda yayi daidai da shekara daya da kwana talatin da tara, inda ya ziyarci kasashe talatin da uku cikin wa’adinsa na farko a ofis.

Kasar da yafi yawan ziyarta dai ita ce kasar Ingila, inda ya dauki tsawon kwana 217 akasari saboda neman lafiya da kuma ganawa da shuwagabannin kasashen da kasar ta Ingila t arena kana kuma da wasu lamuran gwamnati.

Buhari ya kwashi tsawon shekara daya da kwana talatin da tara a kasashen waje cikin shekara uku da wata goma
Muhammadu Buhari
Source: Facebook

KU KARANTA:Kungiyar kare yancin dan adam ta soki CP Wakili bisa kama mataimakin gwamnan Kano

Kasa ta biyu kuwa itace, kasar Amurka inda ya kwashi tsawon kawanaki arba’in da daya amma a lokuta daban-daban ya ziyarci wannan kasa. Ya hadu da Shugaba Obama da kuma Donald Trump a lokuta daban-daban sa’anan kuma ya halarci taron majalisar dinkin duniya na 70, 71, 72 da kuma 73.

Kasar Faransa itace kasa ta uku cikin jerin kasashen da Buhari yafi yawan ziyarta, ya kwashi tsawon kwanaki 14 ne a kasar, yayinda kasar China ke bi mata a jerin gwanon inda ya kwashi tsawon kwanaki 13, kasar Jordan na nan a mataki na biyar inda yake da kwana takwas kacal.

Wasu daga cikin kasashen da shugaban yaje cikin shekaru uku da yan watanni wadanda har yanzu ake kan sake dubawa sun hada da, Dubai; Morocco; Jamus; Afrika ta kudu; Saudiya; Indiya; Chadi; Kenya; Turkiya; Poland da kuma Malta.

Sauran kuwa sun hada da; Habasha; Mauritaniya; Holland; Togo; Benin; Kotdebuwa; Iran; Equitorial Guinea; Kamaru; Ghana; Nijar; Gambia; Misra; Katar; Mali da kuma Sudan. Shugaban kasan bai ziyarci kasa ko daya ba yankin Amurka ta kuda.

Banda fita neman lafiya, dukkanin ziyarar da shugaban ya kai, yayita ne a saboda kawo karshen matsalar tsaro, tattalin arziki, kasuwanci da kuma fada da cin hanci da rashawa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel