Da dumi dumi: 'Yan Boko Haram sun kashe mutane 11

Da dumi dumi: 'Yan Boko Haram sun kashe mutane 11

- 'Yan ta'addar Boko Haram sun kai wani mummunan hari a wani kauye a cikin kasar Kamaru, inda suka kone garin kuma suka kashe mutane 11, suka jikkata da yawa daga cikin mazauna garin

- Rahotanni sun nuna wanne nan mummunan hari da kungiyar ta kai a cikin watannin nan

'Yan ta'addar Boko Haram sun sanyawa wani kauye wuta a kasar Kamaru, sannan sun kashe mutane 11, a lokacin da suke bacci da daddare, in ji wani jami'an tsaron kasar.

"Yan Boko Haram din sun kai farmakin da cikin dare a yankin Tchakamari. Harin ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 11," wata majiya mai karfi ta bayyana hakan.

Da dumi dumi: 'Yan Boko Haram sun kashe mutane 11

Da dumi dumi: 'Yan Boko Haram sun kashe mutane 11
Source: Depositphotos

Wannan shine mummunan hari da 'yan ta'addar Boko Haram din su ka kai a 'yan watannin nan a kasar Kamarun. An dauke gawarwakin wadanda suka kashe din, inda kuma suka sanyawa garin wuta.

Wadanda suka kashe din sun hada da yara da tsofaffi, inda suka kai harin da misalin karfe 10 na dare, sannan suka kai misalin karfe 1 na dare suna kone kauyen.

KU KARANTA: Ya datse hannunshi, saboda ya yi kuskure wurin kada kuri'a

An fara rikicin Boko Haram ne a shekarar 2009 a Najeriya, sannan sun kashe sama da mutane 27,000, sannan sun raba sama da mutane miliyan 2 da gidajen su.

Yanzu haka rikicin ya shafi kasashen da suke makwabtaka da Najeriyan, irin su Nijar, Chad da kasar Kamaru.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel