Zamfara: Dakarun Soji sun kashe 'yan bindiga guda 7

Zamfara: Dakarun Soji sun kashe 'yan bindiga guda 7

- Dakarun sojin hadin guiwa sun samu nasarar kashe 'yan bindiga guda bakwai, sannan sun kama guda uku a jihar Zamfara

- Rahotanni sun nuna cewa 'yan bindigar sun fara guduwa daga jihar suna shiga wasu jihohi

Rundunar sojin Najeriya tare da hadin guiwar 'yan kungiyar sa kai, sun kashe 'yan ta'adda guda bakwai a kauyen Aljumma Fulani da kauyen Ketare da ke jihar Zamfara.

A wata sanarwa da jami'in hukumar sojin a fannin yada labarai ya fitar, Major Clement K. Abiade, ya ce sojojin sun yi wata arangama da 'yan ta'addar wadanda suka zo musu da yawan gaske, amma sabida jajircewa irin ta rundunar ya sa sai da suka sanya 'yan bindigar suka tsere su ka bar sansanin su da kayayyakin su wadanda dakarun suka sawa wuta.

Zamfara: Dakarun Soji sun kashe 'yan bindiga guda 7

Zamfara: Dakarun Soji sun kashe 'yan bindiga guda 7
Source: Twitter

Major Abide ya ce, a yayin gamuwar ta su, sun samu nasarar kashe mutane bakwai daga cikin su, yayin da wasu suka ranta a na kare da raunuka a jikinsu.

Sai dai kuma 'yan bindigar sun kashe soja daya, yayin da sojoji da 'yan kungiyar sa kai guda 6 suka ji raunika.

Dakarun sun samu nasarar kwato makamai masu yawa, wadanda suka hada da bindigogi, harsashi, da kuma babur guda bakwai.

KU KARANTA: 'Yan ta'addar jihar Zamfara sun fara kaura suna shiga wasu jihohi

Hakazalika, dakarun da suka je kasuwar Kara da ke karamar hukumar Shinkafi a yankin jihar Sokoto, sun samu nasarar cafke wani dan leken asiri, wanda ta sanadiyyar shi ne ya sa aka kama 'yan bindiga guda uku.

Wadanda aka kama din sun hada da Lawali Dendenisu Na-mansu, Kabiru Kamarawa daga kauyen Kamarawa da ke cikin karamar hukumar Shinkafi sai kuma Muhammad Sani daga kauyen Indiri.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel