Ya datse hannunshi, saboda ya yi kuskure wurin kada kuri'a

Ya datse hannunshi, saboda ya yi kuskure wurin kada kuri'a

- Wani mutumi ya datse hannun da ya yi amfani da shi ya kada kuri'a, saboda kuskuren da ya yi ya zabi jam'iyyar da ba ita ya ke so ba a kasar Indiya

- Ana sa ran sama da mutane miliyan 900 ne za su kada kuri'a a wannan babban zaben da ake gabatarwa a fadin kasar ta Indiya

Wani mutumi ya datse dan yatsansa, bayan ya gano cewa ya tafka kuskure wurin kada kuri'a, inda ya zabi jam'iyyar da ba ita ya ke so ba.

Lamarin ya faru ne a kasar Indiya da yake yankin nahiyar Asiya, a yayin da ake gabatar da babban zabe a kasar.

Mutumin wanda ya bayyana sunansa da Pawan Kumar ya bayyanawa manema labarai cewa kuskure ne ya saka ya zabi jam'iyya mai mulki a yanzu, wato jam'iyyar Bharatiya Janata Party(BJP).

Ya datse hannunshi, saboda ya yi kuskure wurin kada kuri'a

Ya datse hannunshi, saboda ya yi kuskure wurin kada kuri'a
Source: Facebook

Ya bayyana cewa ya so ya zabi wata jam'iyya ce da ke a yankinsu, amma sai kanshi ya rude ya rasa jam'iyyar saboda yawan alamomin jam'iyyu masu kama daya a na'urar kada kuri'ar.

Ana amfani da wani fenti a goga a jikin dan yatsan da mutum ya yi zabe da shi, wadda ya ke daukar lokaci mai tsawo bai goge ba.

Pawan ya ce ya yi zaben shi ne a ranar Alhamis dinnan a birnin Bulandshahr da ke yankin arewacin jihar Uttar Pradesh.

KU KARANTA: An sanya wa biri kwakwalwar mutum

Wannan shine zango na biyu da za ayi a babban zaben kasar ta Indiya.

"Jam'iyyar da na so na zaba alamar giwa ce a jikinta, amma sai na rude na je na zabi jam'iyya mai alamar fure," in ji Pawan.

Hoton jam'iyya ba karamar rawa ya ke takawa ba a zaben kasar Indiya, saboda ita ce hanya daya da masu kada kuri'a na kasar suke bambance jam'iyyun kasar, musamman ma idan aka yi la'akari da yawan marasa ilimi da suka cika kasar.

Akalla mutane sama da miliyan 900 ne zasu kada kuri'unsu a babban zaben, hakan ne ya sa zaben ya zama mafi girma a tarihin duniya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel