Yan majalisa sun dage zama bayan karbar rahoto kan kasafin kudi har zuwa bayan hutu ista

Yan majalisa sun dage zama bayan karbar rahoto kan kasafin kudi har zuwa bayan hutu ista

-An dage zaman majalisa izuwa bayan hutun ista

-Sai bayan hutun ista zamu duba rahoton kasafi, inji yan majalisar dokoki ta kasa

A jiyane sanatoci da yan majalisar wakilai suka amshi rahoton kasafin kudi na shekarar 2019 daga hannun kwamitin kasafin na majalisun guda biyu. A majalisar dattijai yakamata ace an kawo wannan rahoton ne ranar Alhamis amma hakan bai samu ba saboda rashin kammala aiki akansa da kwamitin baiyi ba.

Mako biyu da suka wuce ne shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki ya sanar cewa rahoton kasafin kudin zai kasance gaban majalisar a ranar 16 ga watan Afrilu wanda yayi daidai da ranar Talatar da ta wuce. Sai dai shima hakan bai yiwu ba.

Sanatoci da yan majalisa sun dage zama bayan karbar rahoto kan kasafin kudi har zuwa bayan hutu ista

Majalisar dokoki
Source: Depositphotos

KU KARANTA:Yan bindiga sun kashe mutum daya a wani kauye dake Jigawa

Sai jiya ne a zaman da majalisar tayi, shugaban kwamitin kasafi na majalisar dattijai wato Senata Mohammed Danjuma Goje (APC, Gwambe), ya mika wannan rahoto a gaban majalisar da misalin karfe uku da rabi na rana.

Anyi tunanin cewa majalisar za ta duba wannan rahoton a ranar, sai dai kuma a daidai lokacin ne majalisar ta dage zaman nata har zuwa ranar Laraba mai zuwa. Shugaban majalisar shine yayi wannan sanarwa inda yake cewa majalisa ta dage zama har zuwa Laraba 24 ga watan Afrilu domin hutun bikin ista.

A majalisar wakilai kuwa, kwamitin kasafin ya gabatar da wannan rahoto gaban majalisar, mai taken ‘Rahoton kasafin 2019’ wanda shugaban kwamitin mai suna, Mustapha Dawaki (APC, Kano) ya mika yayinda mataimakin kakakin majalisar, Yusuf Lasun (APC, Osun) ya karba.

Duk da cewa Dawaki bai bada cikakken bayani akan abinda rahoton ya kunsa ba, amma dai ya shaidawa yan jarida cewa abu na gaba akan rahoton zai biyo bayane idan an dawo hutun bikin ista a ranar Talata mai zuwa wato 23 ga watan Afrilu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel