Wata mata ta hada baki da danta, sun kashe mijinta

Wata mata ta hada baki da danta, sun kashe mijinta

- Wani yaro ya yaje garin taimakon mahaifiyarsa, sun kashe babanshi da duka

- 'Yan sanda sun kama matar da dan da laifin kashe maigidan na ta da duka

- Sai dai kuma yaron ya ce tsautsayin ya faru ne a lokacin da yaje ceto mahaifiyarsa daga hannun mahaifin nasa

Hukumar 'yan sandan jihar Neja ta kama wata mata Hafsat Aliyu mai shekaru 50 a duniya, da danta Babangida Usman, da zargin hada baki suka kashe mahaifin yaron mai suna Ali Haruna.

Lamarin ya faru ranar 13 ga watan Afrilu, 2019, a bayan makarantar firemare ta Shango dake karamar hukumar Chanchaga.

Wata mata ta hada baki da danta, sun kashe mijinta

Wata mata ta hada baki da danta, sun kashe mijinta
Source: Depositphotos

Rahotanni sun nuna cewa Usman da mahafiyarsa sun tarar wa mahaifin Usman din a lokacin da suka samu hatsaniya da mahaifiyar ta shi, inda ya lura da cewa mahaifin nasa ya na takurawa mahaifiyar ta sa a lokuta da dama.

A cewarsa, shi kawai ya yi kokarin ya kare mahaifiyarsa ne daga dukan da mahaifinsan ya ke mataa, inda shi kuma ya fadi ya mutu.

KU KARANTA: Kotu ta bada umarnin rataye wasu mutane guda 7

Jami'in hulda da jama'a na hukumarr 'yan sandan jihar, Mohammed Abubakar, shine ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya kara da cewar wadanda ake tuhumar sun amsa laifinsu.

Abubakar ya ce Usman da Mahaifiyarsa sun yiwa marigayin mummunan rauni, wanda ya mutu yayin da aka kai shi asibitin Ibrahim Badamasi Babangida don yi mishi magani, ya kara da cewa za a gurfanar da wadanda ake zargin a kotu bayan sun kammala bincike.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel