Sama da mutane miliyan 60 ne ke fama rashin ilimi a Najeriya - Gwamnatin tarayya

Sama da mutane miliyan 60 ne ke fama rashin ilimi a Najeriya - Gwamnatin tarayya

- A kokarin da gwamnatin tarayya ta ke na yaki da jahilci, ta ce za ta gina cibiyoyin yaki da jahilci guda 104 a fadin kasar nan

- Sama da mutane miliyan 60 ne ke fama da rashin ilimi a fadin kasar nan

Gwamnatin tarayya ta ce kusan mutane miliyan 60 ne a Najeriya ba su da ilimi, inda ta tabbatar da cewa makarantun yaki da jahilci za su taimaka matuka wurin rage marasa ilimi a kasar.

Sakataren ma'aikatar ilimi na tarayya, Sonny Echono, shi ne ya bayyana hakan a jiya a wata kwalejin tarayya da ke Otobi, a lokacin da aka gabatar da cibiyar yaki da jahilci ta yankin arewa ta tsakiya.

Sama da mutane miliyan 60 ne ke fama rashin ilimi a Najeriya - Gwamnatin tarayya

Sama da mutane miliyan 60 ne ke fama rashin ilimi a Najeriya - Gwamnatin tarayya
Source: UGC

Sakataren ya bayyana rashin jin dadin shi akan yadda yawan marasa ilimi ke karuwa a kasar nan, ya kara da cewa karuwar marasa ilimin a kasar nan abu ne mai ban tsoro.

A cewarsa, cibiyoyin yaki da jahilci guda 104 da za a gina a fadin kasar nan za a yi su ne da nufin rage yawan marasa ilimi a kasar nan, ya kara da cewa gwamnatin tarayya ta fito da wannan tsarin ne saboda yaki da jahilici.

KU KARANTA: Bayan 'yan matsalolin da shafin ya fuskanta, yanzu haka shafin hukumar kwastan ya fara aiki

Ya bayyana cewa shirin zai koyar da al'umma ilimin kimiyya da fasaha, da kuma lissafi domin sanin hanyoyin magance kalubale na rayuwa.

Shugaban makarantar sakandaren, Mista Amudipe Gabriel, ya yaba wa sakataren ma'aikatar ilimin da irin kokarin da ya yi don tabbatar da cewa shirin ya fara aiki, sannan kuma ya yaba mishi da mayar da makarantar shi cibiyar yaki da jahilici ta yankin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel