Yan bindiga sun kashe mutum daya a wani kauye dake Jigawa

Yan bindiga sun kashe mutum daya a wani kauye dake Jigawa

-Yan fashi sun kai hari a kauyen Garin Maidawa dake Jigawa inda suka kashe mutum daya

-Harin ya aukune cikin dare, da misalin karfe biyu da rabi nda mutane da dama suka samu rauni

A jiya ne wasu yan bindiga suka kashe mutum daya tare da raunana wasu mutum tara a kauyen Garin Maidawa dake karamar hukumar Dutse dake jihar Jigawa. Yan bindigan da suka kai kimanin mutum goma sun kwashi tsawon sama da awa biyu suna wannan aika-aika.

Daya daga cikin matar wanda harin ya rutsa dashi, Rahanatu Husaini tace, yan bindigan sun fado masu gida misalin karfe biyu da rabi na dare inda suka tambayi maigidan nata kudi. Mijinta mai suna Husaini Liman baiyi masu gardama ba ya dau kudin ya basu kana kuma suka harbeshi duk da haka.

Yan bindiga sun kashe mutum daya a wani kauye dake Jigawa

Yan bindiga
Source: Twitter

KU KARANTA:Najeriya na cikin matsanancin hali, OPC ta fadawa Shugaba Buhari

Anyi gaggawar kai mijin nata asibitin koyarwa na Aminu Kano. Ta kara da cewa wani mutum daya da ya fito domin kawo dauki shima an harbeshi, yayinda suma wasu yara uku da ma wasu mutane da dama wadanda sukayi kokarin kawo agaji duk sun samu raunuka sakamakon harbin bindiga.

Yayinda da muke zantawa da Kwamishinan yan sandan jihar, Bala Zama Senchi yace, “Kasancewar kauyen dan karami wanda baida tasahar yan sanda ko kuma hanyar da mota zata iya bi, ya samu harin yan fashine wadanda suka zo domin suyi fashi ga mutanen kauyen.

“Ba zan iya baku cikakken bayani akan aukuwar lamarin ba, saboda labarin dake garemu akan lamarin kalilan ne a halin yanzu. Sai dai kuma, mun tura da kwararrun jami’ai masu yaki da yan fashi da makami (SARS) wannan kauyen, inda kuma na basu umurmin cewa suyi bincike a wannan kauyen har sai sun kama masu laifin.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel