An kama karuwai sama da 30 a Abuja

An kama karuwai sama da 30 a Abuja

- An fara rufe gidajen rawa a Abuja, bayan korafin da mazauna yankunan suke kaiwa hukuma

- A jiya ne aka rufe wani katafaren gidan rawa dake unguwar Utako cikin birnin Abuja

- An kama karuwai sama da talatin kuma a gidan rawan, wanda a yanzu haka suna hannun hukuma

A ranar Larabar nan ne hukumar tsaro a babban birnin tarayya ta kai hari wani wurin casu mai suna (Caramelo Night Club), inda ta kama fiye da karuwai 30.

Sannan hukumar kuma ta cire kofar shiga gidan rawan, don hakan ya zama gargadi ga sauran gidajen rawa da ke fadin birnin Abuja.

Da yake jawabi a wani taron manema labarai akan kamen da suka yi, shugaban kula da tsarin gine - ginen birnin Abuja, Malam Umar Shu'aibu, ya ce gwamnati ba za ta taba yarda da mayar da gine - gine wadanda aka yi su ba akan ka'ida ba zuwa gidan rawa.

Shu'aibu ya ce irin wannan gidajen rawan suna zama barazana ga al'ummar yankin, sannan kuma suna kawo damuwa da takura ga mutanen da ke zama a yankin wurin.

An kama karuwai sama da 30 a Abuja

An kama karuwai sama da 30 a Abuja
Source: Facebook

A cewarsa, "Babu tsarin gidajen rawa a yadda aka tsara gina birnin Abuja, sannan kuma gidan rawan da suka kai wa harin ba a gina shi akan tsarin gidan rawa ba, kamar yadda shaidu suka nuna."

Ya kara da cewa: "Za a rufe gidan rawan, sannan za a mayar da wurin asibiti, kamar yadda aka nu na tun farkon ginin wurin."

Hukumar ta samu korafe-korafe daga mazauna yankin da gidan rawan ya ke, inda suke bayyana cewa ana shiga hakkin su.

KU KARANTA: Kotu ta bada umarnin rataye wasu mutane guda 7

Har ila yau, Sakataren harkokin hukumar, Hajiya Safiya Umar, ta ce wajibi ne a kama wanda ke da gidan rawan domin zartar da hukunci akan shi, sannan kuma ta nuna bacin ranta akan karuwan da aka kama.

Ta ce da yawansu sun fito daga gidaje masu arziki, kuma wadansu daga cikin su ma, suna da aure hadda yara.

Sai dai ta nuna cewa an kai karuwan asibitin Wuse, domin likita ya duba su, sannan daga bisani za a kai su cibiyar ladabtar da masu kunnen kashi, inda za su yi watanni uku suna koyon sana'o'i daga nan kuma za a basu jari don lura da kansu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel