Hukuncin Onnoghen nasara ce ga yakin cin hanci da rashawa - Fadar shugaban kasa

Hukuncin Onnoghen nasara ce ga yakin cin hanci da rashawa - Fadar shugaban kasa

A daren jiya Alhamis, fadar shugaban kasa ta yi tsokaci kan hukuncin da kotun CCT yanke kan tsohon shugaban alkalan Najeriya, Walter Onnoghen, inda ta ce wannan babban nasarace ga kudirin gwamnatin shugaba Buhari.

Magana kan aka, mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu, ya bayyana cewa sakamakon shari'ar Onnoghen ya nuna cewa babu ruwan doka da girma kujerar mutum ko matsayinsa.

Hadimin shugaban kasa ya ce amfanin doka shine ya kama duk wanda yayi ba daidai ba kuma doka bata san girma kowa ba.

KU KARANTA: Zababbun yan majalisa 164 sun bayyana goyon bayansu ga Femi Gbajabiamila

Yace: "Yaki da cin hanci da rashawa abu ne da ya game kowa kuma ba'a tsarashi ba don musgunawa wani ba don banbancin siyasa ko wani abu."

"Da sunar doka ta baci idan marasa galihu, talakawa da marasa karfi kadai take kamawa. Kasashe na samun nasara ne idan doka tayi aiki kan kowa."

"Ba za'a samu nasara kan yaki da cin hanci da rashawa ba idan masu fada a ji suna sullubewa saboda karfinsu da mutanen da suka sani. Ba za ka iya yaki da rashawa ba idan ka bari rashin gaskiya ya cigaba da gudana saboda doka ba zatayi aiki ba idan rashin gaskiya na gudana."

Shehu ya kara da cewa wannan hukuncin zai zama darasi ga jama'a cewa yaki da rashawa bata bar kowa ba. ko mutum dan siyasa ne, alkali ne, ma'aikacin gwamnati ne ko yana rike da wani matsayi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel