Yawan ta'ammali da gishiri na haifar da rashin lafiyar Hanta a jikin dan Adam

Yawan ta'ammali da gishiri na haifar da rashin lafiyar Hanta a jikin dan Adam

Wata kwararriyar likita a fannin lafiyar bil Adama wajen amfani da sunadarai, Dakta Onyekachi Onubogu, yayin kira ga al'ummar Najeriya ta ce yawatar amfani da sunadarin dandano na gishiri ya na haifar da mummunar barazana ga lafiyar bil Adama.

Yawan ta'ammali da gishiri na haifar da rashin lafiyar Hanta a jikin dan Adam

Yawan ta'ammali da gishiri na haifar da rashin lafiyar Hanta a jikin dan Adam
Source: UGC

Dakta Onubogu yayin shawartar al'ummar Najeriya a kan saukaka ta'ammali da sunadarin gishiri, ta ce yawaitar amfani da gishiri ya na haifar da mummunar barazana ga lafiya ta lalacewar Hanta ta jikin bil Adama.

Kwararriyar lafiyar ta bayyana hakan ne a yayin kaddamar da wani sabon sunadarin dandano na dunkulen Terra a jihar Legas. Ta ce yawaitar amfani da sunadaran dandano da kuma gishiri su na haifar da barazana ta rashin lafiyar koda da kuma cutar hawan jini.

Ta ce kada al'umma su rudu da son jin dadin dandano a kan harsunan su domin kuwa ingatacciyar lafiya ita ce jari kuma mafi girman arziki ga kowane bil Adama.

KARANTA KUMA: An nada Namadi Sambo shugaban kwamitin amintattu na Jami'ar Baze

Kazalika kwararrun lafiya sun yi gargadi a kan yawaita shan ruwa domin karfafuwar lafiya da ingancin ta ta hanyar wanke duk wasu gurbatattun sunadarai da suka makale a Hanta da kuma Koda ta jikin bil Adama.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel