Da duminsa: Ba zan amince da wannan hukuncin ba - Onnoghen ya daukaka kara

Da duminsa: Ba zan amince da wannan hukuncin ba - Onnoghen ya daukaka kara

Tsohon shugaban Alkalan Najeriya, Walter Nkanu Onnoghen, ya bayyana rashin amincewarsa da shari'ar da alkalin kotun CCT, Danladi Umar, ya yanke na tabbatar da zargin da ake masa na rashin bayyana wasu dukiyoyinsa.

A karar da ya shigar kotun daukaka kara, Onnoghen yana kalubalantar gwamnatin tarayya. Karar yace:

"Ka sani cewa wanda ke daukaka wannan, Walter Onnoghen Nkanu Samuel, bai amince da shari'ar kotun CCT karkashin jagorancin Coram Danladi Umar, William Atedze da Julie A Anakor a ranar 18 ga watan Aprilu, 2019 inda suka yanke hukuncin cewa kotun na da hurumin sauraron karar da kuma yanke hukunci akai."

A daya daga cikin zargi 16 da ake masa, Walter Onnoghen ya ce CCT ta yi kuskure inda tayi watsi da karar kalubalantar huruminta.

Kana kotu ta yi kuskure wajen watsi da karar da ta shigar na bukatar Alkalin kotun ya sauka daga kujerarsa saboda yana nuna bangaranci.

KU KARANTA: Sata ta saci sata; Babana ya saci N3.8m daga N4.5m da na ansa a matsayin kudin fansa- Mai garkuwa da mutane

Justice Onnoghen, ya bukaci kotun daukaka kara ta yanke hukuncin cewa CCT ba tada ikon gurfanar da shi. Sannan ta soke dukkan zarge-zargen kuma ta wankeshi.

Kotun hukunta ma'aikatan gwamnati wato CCT ta yanke hukunci kan tsohon shugaban alkalan Najeriya, Walter Onnoghen, kan zargin rashin bayyana dukkan dukiyoyinsa kamar yadda dokar CCB ta tanada.

Alkalin kotun CCT, Danladi Umar, ya tabbatar da zargin da ake masa kuma yanke hukunci uku kan Onnoghen inda yace:

1. A saukesa daga kujerar Alkalin Alkalai

2. An haramta masa rike wani kujerar mulki na tsawon shekaru goma

3. An kwace dukkan kudaden da aka samu cikin asusun banki biyar ya ki bayyanawa saboda ya gaza bayyana yadda ya samesu

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel