Kisan fararen hula: Rundunar sojin sama ta mayar wa sarakunan Zamfara martani

Kisan fararen hula: Rundunar sojin sama ta mayar wa sarakunan Zamfara martani

Rundunar sojin sama ta kasa (NAF) ta mayar da martani a kan fitar da jerin sunayen mutanen da sarakunan jihar Zamfara suka zarge ta da kashe wa yayin wani luguden wuta da tayi a sansanin 'yan bidigar da suka addabi jihar da kisan mutane da garkuwa da su.

Rundunar ta ce ba ta saki bam a maboyar 'yan ta'addar ba.

Kungiyar sarakunan jihar Zamfara, ta hannun shugabanta, sarkin Bungudu, Alhaji Hassan Attahiru, ta fitar da wani jerin sunayen fararen hula da tayi zargin cewar rundunar sojin sama ce ta kashe su yayin wani samame, ta sararin samaniya, da ta kai yankin jihar Zamfara.

Bayan sakin sunayen mutanen a ranar Laraba, shugaban rundunar sojin sama, Air Marshal Sadique Abubakar, ya kafa kwamitin bincike, a karkashin mataimakinsa, da zai bi kwakwaf a kan zargin da sarakunan suka yi, a cewar NAF.

Kisan fararen hula: Rundunar sojin sama ta mayar wa sarakunan Zamfara martani

Sadique Abubakar
Source: Twitter

Da yake magana da manema labarai a hedikwatar NAF da ke Abuja, darektan yada labarai da hulda da jama'a, Kwamado Ibikunle Daramola, ya yi watsi tare da karyata zargin cewar NAF tayi amfani da bam a jihar Zamfara.

DUBA WANNAN: Abinda ya sa kasashen da suka cigaba basa son taimakon Najeriya - Buhari

Ya ce duk da NAF za ta gudanar da bincike a kan dukkan sunan da sarakunan suka fitar, dakarun rundunar ba za su tsagaita da aikin tabbatar da tsaron lafiya da dukiyar al'umma a jihar Zamfara ba.

Daramola ya ce dakarun NAF ba sa kai farmaki ba tare da gudanar da bincike domin tabbatar da bayanan da aka ba su a kan mafakar 'yan ta'adda ba, ya ce ko da sun kai farmaki basa amfani da manyan makamai wajen kisan 'yan bindigar.

Ya kafe kan cewar babu yadda za ai rundunar sojin saman tayi amfani da bam a wurin da zata iya amfani da kananan makamai domin murkushe 'yan ta'adda.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel