Wike ya dakatar da shuwagabannin kananan hukomi 12 saboda kin hallartar wani aiki mai muhimmanci

Wike ya dakatar da shuwagabannin kananan hukomi 12 saboda kin hallartar wani aiki mai muhimmanci

-Wike ya dakatar da shuwagabannin kananan hukumomi goma sha biyu, kana kuma ya aikawa majalisar dokokin jihar takarda akan hakan

Gwamnan jihar Rivers, Nyesom WIke ya dakatar da shuwagabannin kananan hukomi 12 a dalilin rashin hallartar wani aiki mai matukar muhimmanci. Zancen da ya fito daga bakin hadimin gwamnan mai suna Simeon Nwakaudu ya tabbatar da wannan batu inda yake cewa dakatarwar zata fara aikine da gaggawa.

Kananan hukomin da abin ya shafa sun hada da, Okrika, Emohua, Abua, Degema, Khana, Gokana, Ahoada ta gabas, Ikwerre, Eleme, Andoni, Omuma da kuma Ogu. A cewar tasa, “Gwamnan jihar Rivers Nyesom ya dakatar da shuwagabannin kananan hukumomi goma sha biyu.

Wike ya dakatar da shuwagabannin kananan hukomi 12 saboda kin hallartar wani aiki mai muhimmanci

Nyesom Wike
Source: Depositphotos

KU KARANTA:Buhari zai kara kaimi a zango na biyu, inji wata Kungiya

“Shuwagabannin da aka dakatar sun hada da;

-Philomena Kingolo na karamar hukumar Okrika

-Tom Aliezi na karamar hukumar Emohua

-Daniel E.O Daniel na karamar hukumar Abua

-Tony Phimoore na karamar hukumar Degema

-Lahteh Loolo na karamar hukumar Khana

-Paul Kobani na karamar hukumar Gokana

-Ben Eke na karamar hukumar Ahoada ta gabas

-Samuel Nwanosike na karamar hukumar Ikwerre

-Philip Okparaji na karamar hukmar Eleme

-Paul L. Paul na karamar hukumar Andoni

-Christain Nwaiwu na karamar hukumar Omuma

-Erasmus Victor na karamar hukumar Ogu

Gwamna Wike ya tura ma majalisar dokokin jihar da wasikar dakatar da wadannan shuwagabannin kananan hukumomi 12 wanda ke dauke da taken ‘Sanarwar dakatar da shuwagabannin kananan hukumomi 12; a bisa ga tsarin dokoki na jihar Rivers sashe na sittin da hudu uku cikin baka, doka mai lamba biyar.’

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel