Sata ta saci sata; Babana ya saci N3.8m daga N4.5m da na ansa a matsayin kudin fansa- Mai garkuwa da mutane

Sata ta saci sata; Babana ya saci N3.8m daga N4.5m da na ansa a matsayin kudin fansa- Mai garkuwa da mutane

Wani mai garkuwa da mutane, Edidiong Bill, wanda aka fi sani da ‘Barista’, ya bayyana cewa jiya mahaifinshi ya saci kudi daga cikin abinda ya karba a matsayin fansa yayinda da ya kai kudin gida.

Barristan ya bayyana ma manema labarai yayinda yan sanda suka chafke shi cewa, yayi yunkurin garkuwa da mutane 3 amma 1 kawai ya samu nasara akai.

Bisa ga bayanin shi yace, Ya karbi N4.5m a matsayin kudin fansa amma babanshi ya saci N3.8m yayinda ya kawo kudin gida dan ya adana.

KU KARANTA: Buhari ya rattaba hannu kan sabon mafi karancin albashin ma'aikata

Yace, “Nayi garkuwa da wata budurwa a unguwar Akpan Essien a Uyo sannan na ajiyeta a wani kango, Daga baya sai na amsa 4.5m a matsayin kudin fansa."

"Ban cika zama da mahaifina ba amma a ranar, sai na tafi gida da kudin na boye, kawai daga baya nayi la’akari mahaifina ya saci 3.8m daga kudin."

Yan sandan sun bayyana cewa an taba sashi a gidan kurkuku akan irin wannan ta’addancin a shekara ta 2014.

Shugaban yan sandan yace an kama shine yayinda aka kama kungiyar tasu a kauyen Afaha Effiat dake karamar hukumar Etinan.

Yan sandan sunce yana daya daga cikin tantirai masu garkuwa da mutane. Yayi garkuwa da mutane dayawa da kuma fashi a tsakanin gadar Etinan-Uyo da Calabar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel