Kwadayi mabudin wahala: Kotu ta yanke hukunci akan katon da yayi ma kananan yara mata 2 fyade

Kwadayi mabudin wahala: Kotu ta yanke hukunci akan katon da yayi ma kananan yara mata 2 fyade

Wata kotun majistri dake zamanta a garin Ogudu na jahar Legas ta bada umarnin a garkame mata wani katon banza mai shekaru 41, Josiah Bassey bisa tuhumarsa da ake yin a zakke ma wasu kananan yara mata biyu yan gida daya.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wadannan yan mata yan gida daya suna da shekaru uku ne da kuma mai shekaru bakwai, kamar yadda Dansanda mai shigar da kara ya bayyana ma Alkalin kotun, Alkaliya E. Kubeinje.

KU KARANTA: Kalli kyawawan hotunan Aisha Yesufu da mijinta yayin da suke murnar shekaru 21 da aure

Sai duk magiyar da wanda ake kara yayi ma kotu na tayi masa sassauci, Alkaliyar tayi biris dashi, inda tace dolene a daure mata shi a gidan yarin Kirikiri har sai ta samu shawara daga ofishin babban jami’i mai shigar da kara na jahar Legas.

Da yake bayyana ma kotu yadda lamarin ya auku, Dansanda mai kara, Sufeta Lucky Ihiehie ya bayyana cewa Josiah ya aikata wannan aikin ashshsa ne a shekarar 2018 a gidansa dake unguwar Agidi, cikin yankin Alapere na jahar Legas.

Dansandan yace Josiah yana fakewa da sunan yaran makwabtansa suna kai masa ziyara ne, da haka yake samun damar zakke musu, daga bisani ne babbar ta bayyana ma uwarta abinda yake mata, sai itama karamar ta shaida ma mahaifiyar abinda yake mata, da haka aka kamashi.

Daga karshe Dansandan yace laifin da ake tuhumar Josiah dashi ya saba ma sashi na 137 na kundin hukunta manyan laifuka na jahar Legas na shekarar 2015, kuma hukunsa shine daurin rai da rai, kamar yadda doka ta tanada.

Bayan sauraron dukkanin bangarorin biyu, Alkaliyar tace “Saboda girman laifin da ake tuhumarka dashi, b azan iya bada belinka ba, don haka a daureshi a gidan yarin Kirikiri har sai ranar 28 ga watan Mayu don cigaba da sauraron karar.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel