Ba kan ta: Kotu ta tsige Sanatan APC, ta ce dole ya biya albashi da alawus din da ya karba cikin mako 2

Ba kan ta: Kotu ta tsige Sanatan APC, ta ce dole ya biya albashi da alawus din da ya karba cikin mako 2

- Kotu ta tsige Sonni Ogbuoji, mamba a majalisar dattijai daga jihar Ebonyi

- Wata kotun tarayya da ke zaman ta a Abakaliki ne ta tsige sanatan saboda ya canja sheka daga jam'iyyar da aka zabe shi a cikin ta

- Kotun ta umarci Ogbuoji ya bar kujerar sa ta sanata tare da bawa INEC umarnin ta karbe shaidar sa ta cin zabe

Wata kotun tarayya da ke zaman ta a Abakaliki, babban birnin jihar Ebonyi, ta tsige Sonni Ogbuoji, sanata mai wakiltar jihar Ebonyi ta kudu a majalisar dattijai, saboda ya canja sheka daga jam'iyyar da aka zabe shi a cikin ta.

Yanzu haka kujerar sanatan jihar Ebonyi ta kudu a majalisar dattijai ta zama hotiho biyo bayan hukuncin kotun da ya tsige Ogbuoji.

Ogbuoji, mamba a majalisar dattijai, da aka zaba a karkashin inuwar jam'iyyar PDP, ya canja sheka zuwa jam'iyyar APC a shekarar 2018.

Ba kan ta: Kotu ta tsige Sanatan APC, ta ce dole ya biya albashi da alawus din da ya karba cikin mako 2

Sanata Sunny Ogbuoji
Source: Twitter

Kotun da ta tsige dan majalisar, ta bawa hukumar zabe ta kasa (INEC) umarnin karbe takardar sa ta shaidar cin zaben kujerar sanata tare da ba ta umarnin gudanar da sabon zabe cikin gaggawa domin maye gurbin Ogbuoji.

DUBA WANNAN: Kotu ta soke zaben dan majalisar wakilai na APC daga Katsina

A cewar alkalin kotun, Jastis Akintola Aluko, canjin shekar Ogbuoji ya saba da sashe na 68(1) na kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999, wanda ya ce duk dan majalisar da ya canja sheka daga jam'iyyar da aka zabe shi kafin karewar wa'adinsa, zai bar kujerar sa.

Da ya ke yanke hukunci a karar da jam'iyyar PDP ta shigar, Jastis Aluko ya umarci Ogbuoji ya mayar da dukkan albashi da alawus din da ya karba zuwa aljihun gwamnati, kamar yadda masu kara suka bukata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel