An nada Namadi Sambo shugaban kwamitin amintattu na Jami'ar Baze

An nada Namadi Sambo shugaban kwamitin amintattu na Jami'ar Baze

A ranar Alhamis, 18, ga watan Afrilun 2019, Jami'ar Baze da ke garin Abuja, ta yi nadin mukami ga tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Namadi Sambo, a matsayin shugaban kwamitin amintattu tare da wasu mambobi biyar na kwamitin.

Sabbin mambobin kwamitin da za su yiwa jami'ar Baze hidima cikin wa'adi na tsawon shekaru biyar sun hadar da tsohon sakataren gwamnatin tarayya Alhaji Yayale Ahmad, tsohon jakadan Najeriya na dindindin a majalisar dinkin duniya kuma tsohon ministan harkokin kasashen ketare, Ambasada Joy Ogwu.

Tsohon mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo tare da shugaban kasa Muhammadu Buhari
Tsohon mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo tare da shugaban kasa Muhammadu Buhari
Source: UGC

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito,sauran mambobin kwamitin da tsohon mataimakin shugaban kasa zai jagoranta sun hadar da; Dakta Charles Aderemi da kuma mawallafi na jaridar Mainstream, Mista Sam Nda-Isaiah.

Cikin jawaban sa na rantsuwa, tsohon mataimakin shugaban kasa ya ce bai yi wata-wata ba wajen amsar wannan mukami hannu biyu-biyu sakamakon cikar babban buri na rayuwar sa na yiwa Najeriya hidima a bangaren ilimi.

Tsohon mataimakin shugaban kasa Sambo ya ce, zai jajirce tare da gudanar da aiki tukuru wajen bayar da gagarumar gudunmuwa da za ta yi tasiri wajen warware kalabalai na ilimi da ake fuskanta a fadin kasar nan.

KARANTA KUMA: 'Yan Najeriya su juya baya ga Motoci masu amfani da wutar lantarki - Ekweremadu

A na sa jawaban, wanda ya assasa jami'ar Baze, Sanata Yusuf Datti Baba Ahmad, ya ce kwamitin amintattu da aka nada sun kasance mashahuran Mutane a fadin Najeriya da al'umma sun yi amanna da cancantar su ta rike ko wace irin akala ta jagoranci.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel