Sabon karin albashi ya fara aiki ne daga yau - Fadar shugaban kasa

Sabon karin albashi ya fara aiki ne daga yau - Fadar shugaban kasa

Sabon karin mafi karancin albashi zuwa N30,000 da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya saka wa hannu zai fara aiki ne daga yau, 18 ga watan Afrilu, kamar yadda hadimin shugaban kasa, Mista Ita Enang, ya sanar.

Enang, babban mai bawa shugaban kasa shawara a kan harkokin da suka shafi majalisa, ya sanar da hakan ne ga manema labarai a fadar shugaban kasa a Abuja, ya rattaba hannun shugaba Buhari a kan dokar sabon albashin ta maye gurbin tsohuwar dokar mafi karancin albashi.

A cewar sa, dokar yanzu ta tilasta wa dukkan ma'aikatu; na gwamnati da masu zaman kan su, biyan N30,000 a matsayin mafi karancin albashi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel