'Yan Najeriya su juya baya ga Motoci masu amfani da wutar lantarki - Ekweremadu

'Yan Najeriya su juya baya ga Motoci masu amfani da wutar lantarki - Ekweremadu

Kasancewar Najeriya kasa mai arziki na man fetur, majalisar dattawan kasar ta yi kira na nema gami da shawartar al'umma da su karaucewa sayen Motoci na fasahar zamani masu amfani da wutar lantarki kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito.

Mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Ike Ekweremadu, kasancewar Najeriya kasa mai arziki na man fetur, ya yi kira na shawartar al'ummar kasar da su kauracewa sayen Motocin zamani masu amfani da wutar lantarki.

Sanata Ike Ekweremadu

Sanata Ike Ekweremadu
Source: Depositphotos

Ekweremadu ya yi wannan furuci yayin zaman majalisar da aka gudanar a ranar Larabar da ta gabata biyo bayan muhawarar wani kudiri da wakilin shiyyar Bayelsa ta Gabas, Sanata Ben Murray Bruce na jam'iyyar PDP ya shimfida a zauren majalisa.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, Sanata Bruce ya gabatar da muhawara ta kudirin watsi da motoci masu amfani da man fetur daga doron kasa a duniya daga yanzu zuwa shekarar 2035. Ana kuma neman samun karbuwa ta motoci masu amfani da wutar lantarki.

Cikin madogara ta hujjar kudirin da Sanatan jihar Bayelsa ya gabatar, ya ce motoci masu amfani da wutar lantarki sun fi lafiya, dadin mu'amala ta fuskar tattalin dukiya, kuma buga da kari ba su da alaka ta haifar da dumamar yanayi.

KARANTA KUMA: Kujerar shugaban majalisar dattawa: Danjuma Goje ne zabin mu - Kungiyar Arewa maso Gabas

A nasa bangaren, Sanata Ekweremadu ya ce watsi da motoci masu amfani da man fetur zai janyo durkushewar Najeriya ta fuskar karayar tattalin arziki a yayin da man fetur ya kasance babbar madogarar arziki da ta jingina izuwa gare shi.

A yayin da Sanata Bruce ya janye wannan kudirin dindindin daga zauren majalisar dattawa biyo hambara ta Sanatoci da dama, wakilin shiyyar Kano ta Arewa, Sanata Barau Jibrin na jam'iyyar APC, ya ce tursasa karbuwar motoci masu amfani da wutar lantarki a Najeriya ba zai tabbata ba.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel