Yanzu-yanzu: Buhari ya rattaba hannu kan sabon mafi karancin albashin ma'aikata - Majiya

Yanzu-yanzu: Buhari ya rattaba hannu kan sabon mafi karancin albashin ma'aikata - Majiya

Shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannu kan dokan sabon mafi karancin albashin ma'aikatan Najeriya. Jaridar Daily Trust ta samu rahoto.

Majiya daga fadar shugaba kasa ta bayyana cewa Buhari ya rattaba hannunsa ne kan dokar yau.

Shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannun ne ranar Alhamis a birnin tarayya Abuja, kuma hakan ya wajabtawa dukkan ma'aikatu biyan ma'aikata mafi karancin albashin N30,000.

Majalisar dokokin tarayya ta aika takardan doka zuwa ga shugaban kasa ranar 27 ga watan Maris, 2019.

KU KARANTA: Kotun sauraren korefe-korefen zabe ta sallami kara akan Goje

Gabanin zaben 2019, Majalisar dattawa da na wakilai sun amince da N30,000 matsayin mafi karancin albashin da ya kamata a rika biyan ma'aikatan Najeriya.

A farkon wannan makon, ma'aikatan birnin tarayya sun roki shugaban kasa ya taimaka ya rattaba hannu kan takardan mafi karancin albashi saboda jinkirin da yakeyi na tayar da hankulan mutane.

Babban hadimin shugaba Buhari kan majalisar dattawa, Sanata Ita Enang, ya gabatar da jawabi ga manema labarai a fadar shugaban kasa kan tabbaci da gaskiyan wannan lamari ranar Alhamis.

A watan Junairu, shugaba Buhari ya bukaci majalisa ta amince da N27,000 matsayin mafi karancin albashi amma majalisar dokokin tarayya sunce sam, sai an biya ma'aikata N30,000.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel