Nasara ta mu ce a zaben gwamnan jihar Kogi - PDP

Nasara ta mu ce a zaben gwamnan jihar Kogi - PDP

Cikin bugun gaba gami da yakini, jam'iyyar adawa ta PDP na ci gaba da kyautata zato na samun nasara a yayin zaben gwamnan jihar Kogi da za a gudanar a ranar 2 ga watan Nuwamba na 2019 kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Jam'iyyar PDP ta bayyana yakinin ta na samun nasara cikin wata sanarwa da ta gabatar bayan wata muhimmiyar ganawa ta musamman ta masu ruwa da tsaki da ta gudanar a babban ofishin ta da ke garin Abuja a ranar Larabar da ta gabata.

Nasara ta mu ce a zaben gwamnan jihar Kogi - PDP

Nasara ta mu ce a zaben gwamnan jihar Kogi - PDP
Source: Twitter

Uwar jam'iyyar ta yanke shawarar hada kawunan dukkanin mambobin ta wurin guda wajen aiki tare da cimma manufa guda domin tabbatuwar kudirin ta na ci gaban jam'iyyar da kuma inganta jin dadin al'ummar jihar Kogi baki daya.

Yayin gabatar da jawaban sa na bude taro, kakakin jam'iyyar na kasa Mista Kola Ologbondiyan, ya ce jam'iyyar PDP za ta jajirce wajen tabbatar da makamanciyar nasara da ta samu yayin zaben kujerar gwamnonin wasu jihohi da aka gudanar a watan da ya gabata.

Jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, jam'iyyar PDP kamar yadda kakakin ta ya bayyana na ci gaba da fafutikar kwace kujerar mulki daga hannun gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello na jam'iyyar APC. PDP ta jaddada akidar gudanar da tsarkakken zabe na gaskiya da kuma adalci.

KARANTA KUMA: Cin zarafin 'ya'yan ta: PDP ta janye zanga-zanga a jihar Kano

Jam'iyyar PDP yayin zage dantse na karbar ragamar jagoranci a jihar Kogi, ta yi kira na neman maimaicin nasarar da ta samu a zaben gwamnonin jihohin Bauchi, Imo, Ribas, Adamawa, Sakkwato, Bayelsa, Benuwai da sauran su.

Masu ruwa da tsaki na jam'iyyar PDP reshen jihar Kogi da suka halarci taron sun hadar da; Kaftin Idris Wada, Alhaji Ibrahim Idris, Mista Yomi Awoniyi, Sanata Tunde Ogbeha, Cif Patrick Adagba, Mista Samuel Uhotu da kuma sauran kusoshi na jam'iyyar.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Tags:
Online view pixel