Yan sanda sun kama sojan bogi a jihar Delta

Yan sanda sun kama sojan bogi a jihar Delta

-Wani mai karyar cewa shi jami'in sojane ya shiga hannun yan sanda

-Ruwa ya karewa dan kada! yan sanda sun kama wani sojan bogi a Warri dake Delta

Gangamin yan sandan dake Ekpan karkashin karamar hukumar Uvwie dake jihar Delta wacce SP Ibok Asamanyi ke jagoranta, ta samu nasarar kama wani mai karyar cewa shi Manjo ne na sojan Najeriya.

An kama wannan mutum ne mai suna Blessing Emelor a ranar 6 ga watan Afrilu a Warri. Zance daga bakin yan sandan sun ce abin yazo masa ne da rashin sa’a a ranar, yayinda ya umurci wasu kananan jami’an sojin sama dasu harbi wani mutum da yazo wucewa al’amarin da ya kusa sanadiyar mutuwar wannan mutumin.

Yan sanda sun kama sojan bogi a jihar Delta

Blessing Emelor
Source: UGC

KARANTA WANNAN:Yan Najeriya miliyan goma ne zasu amfana da tsarin TraderMoni, inji Osinbajo

A nan kuwa aka kai kara wajen yan sanda cewa ga abinda ya faru, take nan yan sanda basu tsaya ba suka tafi zuwa kama wannan mutum mai ikirarin cewa shi manjo ne amma na karya. Mai magana da yawun yan sandan, ya shaida mana cewa, mutumin ya dade yana shiga irin ta sojoji inda yake aikata duk abinda yaga dama. Ganin cewa mutane ba su san cewa shi din ba sojan gaskiya bane.

A halin yanzu dai wannan mutum yana hannun CID ta jihar inda bayan sun kamala nasu binciken za’a tura shi kotu domin a zartar masa da hukuncin da ya dace dashi, inji ASP Orisewezie.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel