Yanzu-yanzu: Kotu ta yanke hukunci kan Onnoghen, ta bada umurni 3 kansa

Yanzu-yanzu: Kotu ta yanke hukunci kan Onnoghen, ta bada umurni 3 kansa

Kotun hukunta ma'aikatan gwamnati wato CCT ta yanke hukunci kan tsohon shugaban alkalan Najeriya, Walter Onnoghen, kan zargin rashin bayyana dukkan dukiyoyinsa kamar yadda dokar CCB ta tanada.

Alkalin kotun CCT, Danladi Umar, ya tabbatar da zargin da ake masa kuma yanke hukunci uku kan Onnoghen inda yace:

1. A saukesa daga kujerar Alkalin Alkalai

2. An haramta masa rike wani kujerar mulki na tsawon shekaru goma

3. An kwace dukkan kudaden da aka samu cikin asusun banki biyar ya ki bayyanawa saboda ya gaza bayyana yadda ya samesu

Za ku tuna cewa gwamnatin shugaba Buhari tana tuhumtar Jastis Onnoghen da laifin rashin bayyana wasu kudade a asusun banki shida duk da kasancewarsa ma'aikacin gwamnati.

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta umurci hukumar leken asirin kudaden sata wato Nigerian Financial Intelligence Unit (NFIU) da ta daskarar da asusun bankin shugaban Alkalan Najeriya, Jastis Walter Onnoghen, guda biyar.

KU KARANTA: Majalisar wakilai ta mika kudurin neman a bude kwalejin fasaha da kere-kere mallakar Gwamnatin tarayya a Fagge

Wadannan asusu sune:

a. Account No. 5001062686 (Euro) Standard Chartered Bank (SCB)

b. Account No 5001062679 (Pound Sterling) SCB

c. Account No 0001062650 (Dollar) SCB

d. Account No 0001062667 (Naira) SCB, and

e Account No 5000162693 (Naira)

Manyan Lauyoyi 94 karkashin jagorancin Wole Olanipekun sun dira zauren kotun CCT domin kare alkalin alkalai. Sauran lauyoyin sune tsohon ministan shari'a Kanu Agabi, Wole Olanipekun, Chief Chris Uche, Chief Adegboyega Awomolo da sauransu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel