Kotun sauraren korefe-korefen zabe ta sallami kara akan Goje

Kotun sauraren korefe-korefen zabe ta sallami kara akan Goje

-Karar da aka shigar akan Goje ta kawo karshe

-Dan jam'iyar PRP Lamido Umaru Chikaire shine wanda ya shigar da wannan kara

Shugaban kotun na sashen zaben yan majalisar tarayya, Alkali Raphael Ajuwa shine ya sallami wannan kara. “Yace bisa ga la’akari da lokacin da aka ware domin karabar duk wani korafi akan zabe wannan majalisar tasa zata amince da ayi waje da wannan kara.”

Wadanda wannan karar ke hannunsu wato Muhammad Babangida da A.M Inuwa sun tabbatar mana cewa wannan karar dai an shigar da ita a dan lokaci da ya wuce, yayin da suka bada hujjoji guda uku na sallamar karar. Wanda ya shigar da wannan kara yayi wata ganawa ne da iyalansa inda kawunnansa suka matsa mashi da cewa ai lallai sai ya janye wannan kara da ya shigar domin fuskantar kasuwancinsa.

Danjuma Goje

Danjuma Goje
Source: Depositphotos

KU KARANTA:Yan Najeriya miliyan goma ne zasu amfana da tsarin TraderMoni, inji Osinbajo

Masu karar dai sun kasance jam’iyar PRP ne da dan takararta Lamido Umaru Chikaire inda suke karar Danjuma Goje na jami’yar APC da kuma hukumar zabe ta kasa wato INEC. Shi kuwa lauyan dake kariyar wanda ake kara mai suna Haruna Luka cewa yayi, “wannan karar sam bata da tushe balle makama. Saboda haka sallamar karar da akayi ya kara tabbatar da nasarar Danjuma Goje a zaben da ya gabata.”

Hukumar zabe ta bayyana Danjuma Goje a matsayin wanda yayi nasara a zaben dan majalisa mai wakiltar Gwambe ta tsakiya inda ya samu kuri’a 110,116 yayinda Lamido Umaru Chikaire yazo na uku da kuri’a 8,397. Akwai tazara mai nisa tsakanin mutanen biyu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel