Kungiyar COSCON tana so a binciko nasabar Atiku da Shugaba Buhari

Kungiyar COSCON tana so a binciko nasabar Atiku da Shugaba Buhari

Tarin wasu kungiyoyi masu zaman kan-su a Najeriya a karkashin lemar COSCON sun sa baki a game da ce-ce-ku-cen da ake ta faman yi a kan asalin manyan wadanda su kayi takara a babban zaben 2019.

Wannan kungiya ta COSCON ta nemi a gabatar da bincike na musamman da zai fayyacewa Duniya gaskiyar jitar-jitar da ake ji na cewa Alhaji Atiku Abubakar ya fito ne daga kasar Kamaru mai makwabtaka da Najeriya.

Haka zalika kuma ana jefa irin wannan zargi game da asalin shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda wasu ke cewa, ainihin sa mutumin kasar Guinea ne. Wannan ya sa kungiyar COSCON take neman gaskiyar wannan zancen.

KU KARANTA: Atiku bai da irin 'dan-karen ilmin da na ke da shi - Inji Buhari

Kungiyar COSCON tana so a binciko nasabar Atiku da Shugaba Buhari

COSCON na nema a bi diddikin asalin Buhari da Atiku Abubakar
Source: Facebook

Wani babban jami’i na wannan kungiya mai zaman kan-ta, Promise Edomobi, ya koka a kan yadda Bakin wasu kasashe su ke mulkin ‘yan Najeriya tun bayan samuwar ‘yancin kai, game kuma da shiga cikin sauran harkokin kasar.

Edomobi yayi kira da ayi kwakkwaran bincike na musamman da zai nuna kasashen da shugaba Buhari da kuma Abokin hamayyarsa Atiku Abubakar. Wannan zai kawo karshen maganganun da wasu ke yi na musanyan asalin 'yan siyasar.

COSCON tace idan ta tabbata ‘yan siyasar ba ‘yan Najeriya bane, sai a fatattake su a maida su zuwa kasashen su. Chuks Ibegbu na kungiyar Ohanaeze Ndigbo ya nuna takaicin sa kan wannan zargi inda yace abin kunya ne wannan.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel