Igbo na goyon bayan Sanata Ahmad Lawan

Igbo na goyon bayan Sanata Ahmad Lawan

Kabilar Igbo sun nuna goyon bayan su dari bisa dari akan tsayar da Sanata Ahmad Lawan da shugabannin jam'iyyar APC suka yi a matsayin shugaban majalisar dattawa, da kuma tsayar da Hon. Chike Okafor a matsayin kakakin majalisar wakilai

Kungiyar matasan kabilar Igbo, sun nuna goyon bayansu ga Sanata Ahmad Lawan a matsayin shugaban majalisar dattawa, da kuma Hon. Chike Okafor a matsayin kakakin majalisar wakilai.

Kungiyar ta ce ta yanke wannan shawarar ne, bayan irin abinda ta yi a baya da ta goyi bayan zartar da shugabancin a yankin kudu ta yamma.

A cikin sanarwar da aaka fitar a karshen taron da suka yi a garin Umuahia, wanda shugaban kungiyar Ifeanyi Nwaudunna da sakataren kungiyar Magnus Abara, suka sanya hannu a kai, kungiyar ta ce yanzu ta fito domin goyawa jam'iyya baya.

Igbo na goyon bayan Sanata Ahmad Lawan
Igbo na goyon bayan Sanata Ahmad Lawan
Source: Depositphotos

Kungiyar ta bayyana cewa zabar Lawan da Okafor a matsayin shugabanni a Majalisar Dokoki ta kasa za su karfafa yankunan kasar nan da kuma hada kan al'umma don a samu cigaba.

A cewar kungiyar, kasar nan za ta cigaba idan shugaban kasa 'yan majalisu suka hada karfi da karfe wurin gabatar da ayyukan cigaba a fadin kasar nan.

KU KARANTA: Bayan 'yan matsalolin da shafin ya fuskanta, yanzu haka shafin hukumar kwastan ya fara aiki

Kungiyar ta yi kira ga 'yan majalisar dattijai da kuma mambobin majalisar wakilai, musamman na jam'iyyar APC, akan su amince da zabin jam'iyya na shugabannin majalisa.

Majiyarmu LEGIT.NG ta kawo muku rahoton cewa shugaban jam'iyyar APC na kasa, Adams Oshiomole da shugabannin jam'iyya sun amince da Lawan a matsayin shugaban majalisar dattijai na 9.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel