Jami’an tsaro sun yi nasarar kama yan bindiga 15 a Katsina

Jami’an tsaro sun yi nasarar kama yan bindiga 15 a Katsina

- Jami'an tsaro a jihar Katsina sun yi nasarar kama yan fashi da makami 15

- Hakan ya biyo bayan wani mamaya da suka kai mabuyar wasu yan ta’adda a dajin Rugu

- kwamishinan yan sanda, Sanusi Buba ya bayyana hakan a ranar Laraba

Jami’an Operation Puff Adder na jihar Katsina sun yi nasarar kama yan fashi da makami 15, bayan wani mamaya da suka kai mabuyar wasu yan ta’adda a dajin Rugu, kwamishinan yan sanda, Sanusi Buba ya bayyana hakan a jiya Laraba, 17 ga watan Afrilu.

Buba yace an kana masu laifin ne daga kauyukan Garin Waziri da Mahuta da ke karamar hukumar Safana da kauyen Ilella da ke karamar hukumar Batsari na jihar.

Jami’an tsaro sun yi nasarar kama yan bindiga 15 a Katsina

Jami’an tsaro sun yi nasarar kama yan bindiga 15 a Katsina
Source: Depositphotos

Wadanda aka kama sune; Jamilu Abu, Yarima Lawal, Tasi’u Tukur, Abu Audu, da kuma Samaila Abubakar dukkansu yan kauyen Waziri.

Sauran sune, Hamisu Bawa, Yusuf Inusa, Rabe Sani, Bilya Yakubu, Ibrahim Bawa, Yusuf Abdullahi da kuma Abdullahi Ibrahim.

KU KARANTA KUMA: Hukumar hana fasakauri ta cafke Motar Dangote makare da shinkifa 'yar waje

A wani lamari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa Jami’an yan sanda a jihar Katsina sun kama wata matar aure mai suna Safiya Yakubu, kan zargin mallakar wata bindigar Travor-21.

Safiya, ta fada ma manema labarai a lokacin da aka gurfanar da ita, cewa makamin mallakar mijinta mai suna Yakubu ne a kauyen Runka, wanda yake amfani dashi wajen garkuwa da mutane.

Tace mijinta da wasu abokansa sun fada harkar ne na tsawon wani lokaci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel