Buhari ya kira attajirin duniya Bill Gates, ya yaba masa a kan yakar cutar shan inna da kanjamau a Najeriya

Buhari ya kira attajirin duniya Bill Gates, ya yaba masa a kan yakar cutar shan inna da kanjamau a Najeriya

Yayin ribatar fasahar zamani, shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya yi amfani da wayar salula wajen kiran hamshakin mai kudin nan na duniya, Bill Gates, domin yaba masa a kan gudunmuwa ta kyautatawa al'ummomi a fadin duniya.

Buhari tare da Bill Gates

Buhari tare da Bill Gates
Source: UGC

Shugaban kasa Buhari cikin ganawar sa da Mista Gates ta hanyar wayar sadarwa, ya yaba masa musamman a kan gagarumar gudunmuwa da ya ke ci gaba da bayar wa wajen yakar cutar shan inna da kuma kanjamau a Najeriya.

Kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito, shugaban kasa Buhari ya jaddada cewa dukiyar Mista Gates za ta ci gaba amfanar Najeriya da sauran kasashen duniya wajen fidda su zuwa tudun mun tsira.

Mai magana da yawun shugaban kasa Mallam Garba Shehu, cikin wata sanarwa a ranar Larabar da ta gabata ya ce, Mista Gates yayin ganawar sa da Buhari ya taya sa murnar samun nasara ta lashe zaben kujerar sa a karo na biyu.

KARANTA KUMA: Hukumar hana fasakauri ta cafke Motar Dangote makare da shinkifa 'yar waje

Mallam Shehu ya ce Mista Gates ya bayyana farin cikin sa kwarai da aniyya sakamakon kyakkyawar alakar sa da kuma dangataka da ke tsakanin su da shugaban kasa Buhari da ya kasance ginshiki na yaki da rashawa.

Kazalika shugaban kasa Buhari ya bayyana farin ciki dangane a yadda Mista Gates ke sadaukar da dukiyar sa wajen inganta jin dadin rayuwar al'ummomi musamman a nahiyyar Afirka da kuma kasar Najeriya.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel