Likitocin Najeriya sun shiga yajin aiki saboda rashin samun sahihin albashi

Likitocin Najeriya sun shiga yajin aiki saboda rashin samun sahihin albashi

Kungiyar likitocin Najeriya reshen jahar Imo ta sanar da fadawa yajin aiki na sai Baba-ta-ji a ranar Laraba, 17 ga watan Afrilu bisa tirka tirkar dake tsakaninsu da gwamnatin jahar Imo wanda yaki ci yaki cinyewa.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito shugaban kungiyar ta Imo, Dakta Kyrian Duruewure ne ya tabbatar da haka yayin da yake ganawa da manema labaru a garin Owerri, babban birnin jahar Imo, inda yace matsalace ta albashi.

KU KARANTA; Tsuguni bai kare ba: Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da mutum 10 a Kaduna

Dakta Kyrian yace yayin da takwarorinsu na sauran jahohin Najeriya suka fara cin gajiyar kwaskwararren sabon tsarin albashin ma’aikata likitoci, su kuwa gwamnatin jahar Imo tayi biris dasu kamar bata san Allah Ya yi ruwansu ba.

Don haka yace likitocin jahar Imo na kira ga gwamnatin jahar data fara biyan wannan tsarin albashi, kuma ba zasu koma ba har sai ta fara da biyan bashin da taci na watannin baya da bata biya ba.

“Shekara hudu kenan Likitoci basa samun albashinsu cikakke, kashi 70 kawai ake biyanmu, kuma a yanzu haka muna bin bashin albashin watanni 3, wannan bai kamata ba, kuma wannan mugunta ne.” Inji shi.

Sai dai Likitan yace zasu gudanar da yajin aikin ne a mataki mataki, inda likitocin Asibitin koyarwa na jami’ar jahar Imo dake Orlu, likitocin Asibitin kwararru na jahar Imo dake Umuguma da kuma Likitocin cibiyar kula da Asbitoci zasu fara shiga yajin aikin.

Idan kuma gwamnati bata biya musu bukatarsu ba sai su kaddamar da mataki na biyu na yajin aikin, inda kafatanin Likitocin dake aiki a Asibitoci masu zaman kansu da na cibiyoyin kiwon lafiya na gwamnatin tarayya dake jahar zasu shiga yajin aikin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng News

Online view pixel