Lauyan Buhari ya maidawa Atiku Abubakar martani na cewa bai da ilmin Boko

Lauyan Buhari ya maidawa Atiku Abubakar martani na cewa bai da ilmin Boko

Mun samu labari daga Punch cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zargi Abokin takararsa na shugaban kasa a jam’iyyar PDP a zaben 2019 da cewa bai da ilmin da ya dace ya nemi takara a Najeriya.

Shugaba Buhari yana ganin cewa Atiku bai ma da isasshen ilmin da ake bukata kafin a tsaya neman kujerar shugaban kasa. Shugaba Buhari ya kuma nemi Atiku Abubakar ya fito da takardun shaidar karatun da yake ikirarin yayi.

Buhari ya maidawa Atiku martani ne game da korafin da ya kai gaban kotun karar zabe yana nema a soke nasarar da shugaba Buhari ya samu a babban zaben 2019 da sunan cewa Buhari yayi karya game da satifiket din karatun sa.

KU KARANTA: Ministan shari'a ne ke jawowa Buhari matsala - Say No Campaign

Lauyan Buhari ya maidawa Atiku Abubakar martani na cewa bai da ilmin Boko

Buhari yana shakkar Atiku yana ilmin da ya dace ya fito takara
Source: Facebook

Alhaji Atiku ya fadawa kotun da ke sauraron karar zaben shugaban kasa cewa Buhari bai da takardun karatun da yake ikirari. Sannan kuma Lauyoyin Atiku sun ce Buhari yayi karya wajen cike fam din CF001 na hukumar INEC.

Sai dai shugaba Buhari ya fito ya bayyana cewa ya kerewa ‘Dan takarar na PDP wajen harkar ilmin Boko nesa ba kusa ba. Shugaban kasar yayi wannan bayani ne ta bakin wani babban Lauyansa watau Wole Olanipekun (SAN).

Wole Olanipekun wanda yana cikin masu kare shugaba Buhari a gaban kotu, yace shugaban kasar yana da takardun da su ka zarce wadanda ake bukata wajen tsayawa takarar shugaban kasa idan aka yi la’akari da karatun da yayi.

KU KARANTA: Kotu ta dakatar da shari'ar Onnoghen na wani lokaci

Lauyan da ke kare shugaban kasar yake cewa Buhari yayi kwas iri-iri a gida da wajen Najeriya, sannan kuma yace ya fi Atiku ilmi da takardun shaida da kambu da kuma lambar yabo, sannan da kwarewa da sanin makaman aiki.

Lauyoyin shugaban kasar sun nemi kotu tayi watsi da karar da Atiku Abubakar yake yi inda su kace shugaba Buhari bai yi wata karya wajen cike fam din da hukumar INEC ta ba sa mai dauke da jeringiyar inda yayi karatunsa ba.

Masu kare shugaban kasar su kace daga cikin makarantun da yayi karatu akwai:

“Elementary School Daura and Maid’adua – 1948 to 1952;

“Middle School, Katsina – 1953 to 1956;

“Katsina Provincial Secondary School (wanda yanzu ake kira Daura Government College, Katsina) – 1956 to 1961.”

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel