Hukumar hana fasakauri ta cafke Motar Dangote makare da shinkifa 'yar waje

Hukumar hana fasakauri ta cafke Motar Dangote makare da shinkifa 'yar waje

Daya daga cikin manyan Motoci masu dakon kaya mallakin kamfanin fittacen dan kasuwar nan, Aliko Dangote, ta afka tarkon hukumar hana fasa kauri makare da buhunan shinkafa 800 'yar waje kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.

Hukumar hana fasa kauri ta Najeriya, Kwamtam, da ke kula da shiyyar Kudu maso Yammacin kasar nan, ta ce a kwana-kwanan nan ana ci gaba da cafke manyan motoci mallakar kamfanonin cikin gida makare da dako na shinkifa 'yar waje.

Ma'aikatan Hukumar hana fasakauri a bakin aiki
Ma'aikatan Hukumar hana fasakauri a bakin aiki
Source: Depositphotos

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, hakan ya bayu ne yayin da hukumar kwastam ta kama wata babbar mota mai dakon kaya mallakin kamfanin Dangote makare da shinkafa 'yar waje da aka shigo da ita daga kasashen ketare.

Kwanturolan hukumar Kwastam mai kula da reshen na Abuja, Aliyu Muhammad, shi ne ya bayar da shaidar cafke kayan na fasa kauri cikin wata hira yayin ganawar sa da manema labarai a ranar Larabar da ta gabata.

Kazalika hukumar ta Kwastam ta samu nasarar kama wata motar dakon kaya makare da maganin tari Kodin na kimanin Naira Miliyan 240 a babbar hanyar Mil biyu dake yankin Oshodi a jihar Legas.

KARANTA KUMA: Atiku bai taba samun nasarar zabe a kai na ba - Buhari

A yayin da kakakin kamfanin Dangote, Anthony Chiejina ya bayar da shaidar rashin samun wata masaniya a kan wannan harkalla, babban jami'in na Kwastam ya ce hukumar ta samu nasarar cafke kayayyakin fasa kauri da suka hadar da miyagun kwayoyi da kuma shinkafa 'yar waje na kimanin kimanin Naira Miliyan Dari uku a tsakanin watan Fabrairu da Maris cikin jihar Ogun.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel