Yanzu-yanzu: Me ya faru ne? An dakatad da Sharia'ar Onnoghen zuwa karfe 12 na rana

Yanzu-yanzu: Me ya faru ne? An dakatad da Sharia'ar Onnoghen zuwa karfe 12 na rana

Kotun hukunta ma'aikatan gwamnati wato CCT ta dage shari'ar tsohon Alkalin alkalai, Walter Onnoghen, zuwa karfe 12 na rana.

Walter Onnoghen na gurfana gaban kotun ne sakamakon zargin rashin bayyana dukkan dukiyoyin da ya mallaka wanda ya hada da wasu asusunan banki 6 a bankin Standard Chartered.

Alkalin kotun hukunta ma'aikatan gwamnati wato CCT, Danladi Umar, wanda ke jagoranta kwamitin alkalai uku da zasu zanna kan wannan Shari'ar ya bayyana a makon da ya gabata cewa yau za'a yanke hukuncin karshe kan Walter Onnoghen.

KU KARANTA: Yan sanda sun kama sojan bogi a jihar Delta

Lauyoyin Onnoghen da na gwamnati sun rigaya da shiga kotu kafin magatakardan kotun ya sanar da jama'a cewa an dage zama zuwa karfe 12.

A bangare guda, Babban kotun tarayya dake zaune a Kano a ranar alhamis ta kwace kujerar tsohon hadimin Buhari, Kawu Sumaila, na zababben dan majalisar wakilan tarayya mai wakiltar Sumaila/Takai na jihar Kano.

Sumaila, wanda ya kasance hadimin shugaba Buhari kan majalisar wakilai, ya lashe zaben kujerar karkashin jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Kotun ta umurci hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC ta tabbatar da Shamsuddeen Dambazzau matsayin wanda ya lashe zabe.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel