Buhari zai kara kaimi a zango na biyu, inji wata Kungiya

Buhari zai kara kaimi a zango na biyu, inji wata Kungiya

-Shugaba Buhari zai dada jajircewa a zango na biyu

-Za'a ji dadin zangon Buhari na biyu, inji wata kungiyar siyasa

Wata kungiyar siyasa ta Dr. Hajo Sani ta matasa domin zarcewar Buhari, ta fadi hakan inda take cewa Shugaba Buhari zai yi matukar kara kaimi a wanna zangon nasa na biyu a ofis. Kungiyar wacce ta bada wannan sanarwar ta bakin wasu jagororinta ta jaddada wannan magana.

Jagoran kungiyar na kasa mai suna, Salisu Bala Hassan da kuma sakataren kungiyar, Nwafor Odochukwu sun furta cewa yan Najeriya sun zabi Buharin ne saboda sun aminta dashi. Sun kara da cewa, wannan gagarumin goyon baya da Buhari ya samu daga wajen yan Najeriya daliline da zai kara bashi kwarin gwiwar daga kasar zuwa matakin da kowa ke burin ya ga ta kai.

Muhammadu Buhari

Muhammadu Buhari
Source: UGC

KU KARANTA:Majalisar wakilai ta mika kudurin neman a bude kwalejin fasaha da kere-kere mallakar Gwamnatin tarayya a Fagge

Kungiyar kuma ta kara da cewa, duk wani abinda zatayi zai kasance taimakone da kuma shawarwari ga Buhari domin ya samu damar kawo karshen cin hanci dake addabar kasar nan, domin hakan shine zai bamu damar samun ingantaccen jagoranci.

A wani labarin makamancin wannan, Shugaba Buhari ya kira Bill Gates domin yi mashi godiya akan taimakonsa da yake baiwa Najeriya akan kawar da cutar kanjamau. Shugabn ya kara da hakika gwamnatinsu ba zatayi watsi da jama'arta ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel