Yan Najeriya miliyan goma ne zasu amfana da tsarin TraderMoni, inji Osinbajo

Yan Najeriya miliyan goma ne zasu amfana da tsarin TraderMoni, inji Osinbajo

-Mutane miliyan goma zasu amfana da tsarin TraderMoni, a cewar Osinbajo

-Tsarin ciyar da firamare da gwamnatin Najeriya keyi ya isa jihohi talatin a fadin kasar nan

Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo ya bayyana cewa mutane miliyan goma ne zasu amfana da tsarin TraderMoni da kuma N-power a daidai lokacinda wannan gwamnatin ke cigaba da ganin ta gina al’ummarta ta hanyar sama masu aikinyi.

A wani zance daga bakin hadimin Osinbajo, Laolu Akande yace zasu cigaba da kokari domin dorewar ayyuka irin wadannan. Inda ya kara da cewa kudurin Shugaba Buhari na inganta rayuwar al’ummar kasar nan yana nan bai gushe ba, kuma har ila yau abinda suke kokarin tabbbatarwa kenan.

Yemi Osinbajo

Yemi Osinbajo
Source: Facebook

KARANTA WANNAN:Majalisar wakilai ta mika kudurin neman a bude kwalejin fasaha da kere-kere mallakar Gwamnatin tarayya a Fagge

“A wannan matakin na gaba (Next Level) na gwamnatin Buhari, kimanin yan Najeriya miliyan goma ne zasu amfana da tsare-tsaren gwamnati na samar da abinyi ga yan kasar, wadanda suka hada da; tallafin karamar sana’a (TraderMoni), tallafin yin kasuwanci (MarketMoni) da kuma tallafin noma (FarmerMoni). Yayinda kuma rabon tsantsar kudi zai isa zuwa ga mutane miliyan daya masu matukar bukata sai kuma sabbin mutane da za a kara cikin tsarin N-power suma mutum miliyan daya, tsarin na N-power ko shakka babu shi kadaine irinsa baida tamka a fadin Afrika.

“Tsarin ciyar da abinci ga makarantun firamare na gwamnatin kasar nan, shima yana dada bunkasa yayinda ya kasance manufarmu itace ciyar da dalibai miliyan goma sha biyu. A yanzu haka kuwa dalibai miliyan tara da dubu dari biyar ke amfana da wannan tsarin, yaran dai suna tsakanin aji daya ne zuwa uku a matakin firamare. Har wa yau, wannan tsarin ciyarwar daliban firamare na gudana ne a jihohi talatin dake fadin kasar nan, wanda ya samawa masu aikin girke-girke 101,913 aikin yi.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel