Akwai yiwuwar NJC ta sabunta wa’adin CJN Tanko Mohammed

Akwai yiwuwar NJC ta sabunta wa’adin CJN Tanko Mohammed

Punch ta rahoto cewa Majalisar shari’a ta Najeriya ta soma wani babban taro inda za ta za ta zauna na kwana 2 domin tattauna yadda za ta shawo kan wanda za a nada a matsayin Alkalin Alkalan kasar nan.

Kamar yadda labari ya zo mana a yau dinnan 18 ga Watan Afrilu, majalisar koli ta NJC ta fara taro a Abuja a jiya Laraba inda manyan batutuwan da ta ke dubawa su ka shafi nadin Alkalin Alkalai na din-din-din a halin yanzu.

Majiyar jaridar kasar ta bayyana cewa babu mamaki babban majalisar shari’ar ta sabunta wa’adin mai shari’a Tanko Muhammad a matsayin mukaddashin Alkalin Alkalai, har zuwa lokacin da za ayi cikakken nadin kujerar.

Wa’adin Tanko Mohammed zai cika ne a Ranar Alhamis 25 ga Watan Afrilun nan. Dokar kasa ta bada dama ne ga shugaban Alkalai na rikon kwarya da ya rike kujerar na watanni 3 rak, wanda Muhammad zai cika a makon gobe.

KU KARANTA: 'Dan takarar APC yana so Kotu ta soke zaben Dino Melaye

Akwai yiwuwar NJC ta sabunta wa’adin CJN Tanko Mohammed

Mukaddashin Alkalin Najeriya na iya cigaba da rikon kwarya
Source: UGC

Shugaban kasa bai da hurumi a doka da zai nada sabon Alkalin Alkalai ko kuma ya bada dama wanda ke kan matsayin rikon-kwarya da ya cigaba da rike kujerar ba tare da amincewar majalisar shari’a watau NJC ta kasar ba.

A halin yanzu alamu sun nuna cewa kila NJC za tayi na’am da cewa Muhammad zai cigaba da rike wannan mukami har zuwa lokacin da za ayi nadin sabon Alkalin Alkalai na din-din-din bayan dakatar da Walter Onnoghen.

Har yanzu dai majalisar NJC ba ta fara shirin zakulo wanda ya kamata ya gaji Walter Onnoghen da aka cire daga ofis ba, wanda a karshe dole ya rubuta takardar murabus bayan an soma binciken sa a NJC da kuma gaban kuliya.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel