Bauchi: Wata yar bautar kasa ta yanke jiki ta mutu a sansanin NYSC

Bauchi: Wata yar bautar kasa ta yanke jiki ta mutu a sansanin NYSC

- Wata yar bautar kasa, Magdalene Yohanna ta mutu a sansanin yan bautar kasa da ke Bauchi

- Marigayiyar ta yanke jiki ta fadi ne a sansanin yan bautar kasa da ke Wailo yan kwanaki bayan isarta sansanin

- An tattaro cewa marigayiyr tayi wa jami’an NYSC korafin cewa tana da cutar asma sannan cewa ba za ta iya zuwa motsa jikin safe ba amma ba a saurari korafinta ba

Wata yar bautar kasa, Magdalene Yohanna da aka tura jihar Bauchi don bauta na kasarta na tsawon shekara guda ta mutu.

Rahotanni sun kawo cewa marigayiyar ta yanke jiki ta fadi ne a sansanin yan bautar kasa da ke Wailo yan kwanaki bayan isarta sansanin, amma sai ya mutu yan mintuna kadan bayan an kaita asibitin koyarwa na jami’ar Abubakar Tafawa Balewa Bauchi.

An tattaro cewa mumunan al’amarin ya afku ne a filin sintiri, kwanaki hudu bayan yan Batch A sun isa sansanin don yin makonni uku a sansanin Wailo, da ke karamar hukumar Ganjuwa da ke jihar Bauchi.

Bauchi: Wata yar bautar kasa ta yanke jiki ta mutu a sansanin NYSC

Bauchi: Wata yar bautar kasa ta yanke jiki ta mutu a sansanin NYSC
Source: UGC

An ci gaba da rahoto cewa a safiyar ranar 1 ga watan Afrilu, marigayiya Magdalene Yohanna tayi wa jami’an NYSC korafin cewa tana cutar asma sannan cewa ba za ta iya zuwa motsa jikin safe ba amma ba a saurari korafinta ba.

KU KARANTA KUMA: An kama wata matar aure da wani matashi da makamai a Katsina

Don haka duk wani kokari na likitoci domin ceto rayuwarta bai cimma nasara ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel