Ba maganar cire tallafin mai a Najeriya - NNPC ta tabbatar da haka

Ba maganar cire tallafin mai a Najeriya - NNPC ta tabbatar da haka

Kamfanin NNPC ya ce duk irin yadda farashin kayayyakin man fetur ke ta shi, amma hakan ba zai sa a cire tallafin man fetur ba, inda ya tabbatar wa da 'yan Najeriya cewa za a cigaba da sayar da man fetur akan farashin da aka san shi wato naira 145

Duk da karuwar farashin kayayyakin man fetur, za a cigaba da sayar da man fetur akan naira 145, in ji kamfanin man fetur na Najeriya NNPC.

A wata hira da ya yi da manema labarai a waya jiya Laraba a Abuja, babban jami'in hulda da jama'a na kamfanin man fetur din, Mista Ndu Ughamadu, ya ce kamfanin zai ci gaba da amfani da farashin da aka saba amfani da shi na naira 145.

Ba maganar cire tallafin mai a Najeriya - NNPC ta tabbatar da haka

Ba maganar cire tallafin mai a Najeriya - NNPC ta tabbatar da haka
Source: UGC

Ughamadu ya ce, "Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa zata cigaba da sayar da man fetur akan farashin da aka san shi na naira 145 a kowacce lita. Kamfanin NNPC ba zai cire tallafi ba.

A jiya Laraba ne kamfanin NNPC ya musanta kashe dala biliyan 22 na aikin ginin kamfanin LNG.

KU KARANTA: Bayan 'yan matsalolin da shafin ya fuskanta, yanzu haka shafin hukumar kwastan ya fara aiki

A wata sanarwa da ya bayar ga manema labarai a Abuja, Ughamadu ya ce kamfanin ya kashe dala biliyan 1.2 kawai a aikin ginin kamfanin.

Ughamadu ya bayyana cewa kamfanin ya bayar da bayani a kwamitin majalisar wakilai lokacin da ake gabatar da bincike akan kudaden.

A satin da ya gabata ne dai bankin IMF ya bai wa gwamnatin tarayyar Najeriya shawarar ta cire tallafin man fetur, domin ta samu wata hanyar da kudi zai dinga shigo mata, ganin irin yadda kasar ke fama da matsalar tattalin arziki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel