Sojoji sun dakile harin 'yan Boko Haram sun kashe sama da 39

Sojoji sun dakile harin 'yan Boko Haram sun kashe sama da 39

- Dakarun soji sun samu nasarar kashe 'yan Boko Haram 39, bayan sun kawo musu wani hari

- Sai dai kusan sojoji 20 ne suka jikkata sanadiyar harin

Wata rundunar hadin gwiwa ta sojoji ta dakile harin 'yan ta'addar Boko Haram inda suka kashe 'yan ta'adar Boko Haram din guda 39.

Rundunar sojojin hadin gwiwa, ta kashe 'yan ta'addar Boko Haram guda 39, sannan rundunar ta samu nasarar kwace makamai masu yawan gaske.

Sai dai kuma a harin da rundunar sojin ta kai, an samu kusan sojojin 20 wadanda suka ji raunuka

Sojoji sun dakile harin 'yan Boko Haram sun kashe sama da 39

Sojoji sun dakile harin 'yan Boko Haram sun kashe sama da 39
Source: UGC

Mai magana da yawun rundunar, Col. Timothy Antigha, shi ne ya tabbatar da faruwan lamarin, a wata ganawa da ya yi da manema labarai, jiya Laraba a babban birnin tarayya Abuja.

Antigha ya ce rundunar ta samu nasarar kashe 'yan ta'addar masu yawan gaske, bayan 'yan ta'addar sun kawo wa rundunar hari a kusa da Kaura a ranar Talatar nan da ta gabata.

KU KARANTA: Kotu ta bada umarnin rataye wasu mutane guda 7

Ya ce sojojin da suka ji ciwon an dauke su daga wurin da abin ya faru aka wuce da su asibiti, inda a yanzu haka suke karbar magani.

Matsalar Boko Haram dai taki ci taki cinyewa a kasar nan, musamman ma a yankin arewa maso gabas. Rikicin ya yi sanadiyyar mutuwar dubunnan mutane a Najeriya, sannan ya raba miliyoyin mutane da gidajen su, saboda rikicin wanda aka kwashe shekaru masu yawan gaske ana yi amma har ya zuwa yau ba a kawo karshen shi ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel