Mutane na korafe-korafe yayinda karancin ruwa ya kewaye Katsina

Mutane na korafe-korafe yayinda karancin ruwa ya kewaye Katsina

Wani rahoto daga jaridar Daily Trust ya nuna yadda al’umman jihar Katsina ke fama da karancin ruwa a yan makonnin nan.

A bisa ga rahoton, mazauna jihar na arewa maso yamma a yanzu haka suna fuskantar matsi wajen samun ruwa.

Ga Malam Halilu Mohammed da iyalansa, karancin ruwa da zafi sun sa rayuwa yayi masu wahala a gidansu na Kofar Kaura da ke garin Katsina.

Mohammed yace a kullun sai ya siya ruwan N300 daga wajen masu siyar da ruwa, wanda iyalansa ke amfani dashi wajen girki da sauran ayyukan gida.

Mutane na korafe-korafe yayinda karancin ruwa ya kewaye Katsina

Mutane na korafe-korafe yayinda karancin ruwa ya kewaye Katsina
Source: Twitter

Yace fanfunan ruwan da ke gidansa sun yi rotse, saboda hukumar ruwa na jihar basu basu ruwa ba tsawon shekaru hudu da suka gabata tunda ya dawo gidan, bayan an mayar dashi jihar.

Ga Lawal Saidu na Sabuwar Unguwa, yace ruwa ya zamo abu mawuyaci a yankinsa domin a kullun ana siyan ruwa sau biyu. A cewarsa, idan yayi kokarin hada kudin da yake kashewa a shekara, zai yi yawa sosai.

Saidu yace a makon da ya gabata, ya siya ruwan N500 saboda yawan bukata, inda ya bayyana cewa ayi farin ciki a wannan makon domin na N350 ya siya.

Yace lamarin ya munana sosai don a yanzu hatta Almajirai rokon ruwan sha suke yi daga mutane.

KU KARANTA KUMA: An kama wata matar aure da wani matashi da makamai a Katsina

Ga Mohammad Danjuma Katsina wanda ke zama a hanyar Tafawa Balewa, Kofar Kwaya, yace tsawon shekaru 17 da suka gabata bai taba ganin yanayi irin wannan ba.

Yace ana siyar da galan din ruwa a wasu yankunan kan N80, inda yace ba kowa ne zai iya siya ba sannan ga zafi da ake yi, dole za a bukaci ruwa sosai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel