Gwamnati Buhari za ta aro Miliyan $247 domin gyara harkar wutan lantarki

Gwamnati Buhari za ta aro Miliyan $247 domin gyara harkar wutan lantarki

Jaridar Vanguard ta rahoto mana cewa majalisar zartarwa ta Ministocin Najeriya ta amince da a aro wasu miliyoyin daloli domin a gyara wutar lantarki. An cin ma wannan matsaya ne a makon nan.

A zaman taron FEC da aka yi jiya Laraba 17 ga Watan Afrilu, majalisar zartarwa ta tarayya ta bada goyon bayan aro kudi har fam Dala Miliyan 247.3 daga babban bankin nan na Nahiyar Afrika AfDB da kuma kasar Faransa.

Wannan banki da aka kafa domin cigaban kasashen Afrika shi ne zai bada aron Dala Miliyan 150, yayin da wasu Dala Miliyan 50 za su fito daga hannun Africa Grow Together Fund, sai Faransa ta taimaka da Dala Miliyan 20.

Daga cikin wannan kudi da za a samu, Jihar Legas za ta kashe fam Dala Miliyan 20 ne wajen gyara tituna da kuma gina sababbin hanyoyi. Ministar kudi na kasar, Zainab Ahmad ta bayyanawa manema labarai wannan jiya.

KU KARANTA: Mutane na korafe-korafe yayinda karancin ruwa ya kewaye Katsina

Gwamnati Buhari za ta aro Miliyan $247 domin gyara harkar wutan lantarki

Gwamnatin Najeriya za ta karbo aron kudi bayan gargadin IMF
Source: Twitter

A bayanin da Ministar tayi bayan an kammala taron na FEC a fadar shugaban kasa da ke Abuja, ta tabbatar da cewa majalisar Ministoci sun amince da karbo wannan danyen bashi da zai yi amfani wajen inganta wutan Najeriya.

Ahmed take cewa za a kashe kudin ne wajen kafa na’urorin da ke bada wuta da karfin rana a kauyukan Najeriya, wannan zai taimaka wajen ganin mutane 500, 000 a gidaje fiye da 100, 000 sun samu wutan lantarki a fadin kasar nan.

Ministar kudin ta Najeriya tace jami’o’i 8 za su amfana, ban kuma ‘yan kasuwa fiye da 20, 000 da za su ga ribar wannan tsari. Sannan kuma dai akwai wasu ayyuka na hanyoyi da majalisar ta amince duk a jiya.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel