Ko da ana tazarce sau 3 ba zan yi ba don na gaji – Inji Gwamna Wike

Ko da ana tazarce sau 3 ba zan yi ba don na gaji – Inji Gwamna Wike

Mai girma gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya bayyana cewa ya gaji da rike kujerar gwamnan jiha a halin yanzu. Gwamnan yace ko da dokar kasa ta bada dama, da ba zai nemi tazarce bayan 2023 ba.

Gwamna Nyesom Wike ya bayyana wannan ne a lokacin da yake karbar shaidar lashe zaben jihar Ribas da aka yi kwanan nan daga hannun hukumar zabe na kasa mai zaman kan-ta watau INEC, a cikin Garin Fatakawal na jihar.

A jawabin gwamnan na Ranar Talata wajen gabatar masa da satifiket, ya kara nanata maganar zama lafiya a jihar. Nyesom Wike yake cewa babu mahalukin da ya fi karfin jihar. Gwamnan yana kokarin ganin an zauna lafiya.

Har wa yau, gwamnan yayi kira ga mutanen Ribas da babbar murya, a duk inda su ke da su dawo su yi wa jihar aiki. Wike yake kira ga mutanensa da su yi abin da zai taimaki Ribas a duk matakin gwamnatin da su ka samu kan su.

KU KARANTA: APC ta rasa wasu kujerun Majalisar dokoki a Nasarawa

Ko da ana tazarce sau 3 ba zan yi ba don na gaji – Inji Gwamna Wike

Na gaji da wannan aikin na Gwamna – inji Wike na Ribas
Source: UGC

Nyesom Wike yace ba zai cigaba da rike kujerar gwamna har abada ba, inda yace ko da a ce, tsarin mulki zai bada damar ya sake zarcewa, ba zai kuma neman takara ba. Wike yana mai cewa gaba daya ya gaji da wannan aiki na gwamna.

Mista Wike ya kara da cewa a duk rana ta Allah idan ya farka daga barci, ya kan fadawa Mai dakinsa cewa babu wanda ya san abin da zai faru kashegari, haka kuma babu wanda ya isa ya dauki rayuwarsa har sai ranar da Allah yayi.

Gwamnan dai ya godewa Ubangiji da damar da ya samu a rayuwa inda yace idan ya mutu, bai da bukatar a bizne sa a Abuja ko Legas, sai dai a jiharsa ta Ribas, har ya nemi wadanda ya taka a wa’adin sa na farko na baya su yafe masa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel