Tsuguni bai kare ba: Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da mutum 10 a Kaduna

Tsuguni bai kare ba: Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da mutum 10 a Kaduna

Wasu gungun yan bindiga da yawansu ya kai hamsin dauke da muggan makamai sun kai farmaki ga jama’an kauyen Kuriga dake cikin karamar hukumar Chikun ta jahar Kaduna, inda suka yi garkuwa da mutane goma.

Wannan lamari ya faru ne da tsakar daren Talata, inda suka bude wuta irin na mai kan uwa da wabi akan jama’an garin, wanda hakan yasa kowa yayi ta kansa, hatta jami’an kato da gora suka ranta ana kare, kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito.

KU KARANTA: Innalillahi wa inna ilahi raji’un: Anyi jana’izar mutane 16 da yan bindiga suka kashe a Sokoto

Wani mazaunin kauyen Kuriga, Aliyu Bello ya bayyana cewa yan bindigan sun kwashe tsawon awanni uku suna cin karensu babu babbaka inda suka dinga kutsa kai cikin gidajen mutane suna zakulosu, tare da tafiya dasu.

“Da misalin karfe 2 na dare suka shigo, suka shiga harbe harbe, wanda hakan ya jefamu cikin halin rudani da rikicewa, sun yi amfani da diga wajen balla kofofin gidajen jama’a, a haka suka yi awon gaba da maza 6 da mata 4.

“Gaskiya a yanzu kam zamu yi gudun hijira zuwa Birnin Gwari saboda ayyukan masu garkuwa da mutane a yankin nan ya ta’azzara, ba zamu iya cigaba da biyan makudan kudin da suke nema daga wajenmu ba, a yanzu haka yarona da yayana suna hannunsu, kuma miliyan 30 suke nema kafin su sakesu.” Inji shi.

A wani labarin kuma Dakarun rundunar Sojan na musamman sun tarwatsa wasu gungun yan bindiga da suka kaddamar da hare hare a kauyukan Rafi da Dola dake cikin lardin Mada na karamar hukumar Gusau ta jahar Zamfara a ranar Talata, 16 ga watan Afrilu.

Kaakakin rundunar, Komodo Ibikunle Daramola yace sun samu bayanai dake nuna yan bindigan sun fara tattaruwa a kauyukan da nufin kai musu hari, ba tare da bata lokaci ba suka tura Sojoji wanda suka tarwatsa shirin yan bindiga, har ma suka kashe guda biyu daga cikinsu, yayin da sauran suka ranta ana kare dauke da munanan raunuka.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Nigeria

Online view pixel