An kama wata matar aure da wani matashi da makamai a Katsina

An kama wata matar aure da wani matashi da makamai a Katsina

- Yan sanda sun kama wata matar aure mai suna Safiya Yakubu, bisa zargin mallakar bindiga

- Safiya tace makamin mallakar mijinta mai suna Yakubu ne a kauyen Runka, wanda yake amfani dashi wajen garkuwa da mutane

- Hakazalika an kama wani mai suna Jibril Anas da yayi ikirarin mallakar bindiga bias shawarar abokansa domin kare kansa

Jami’an yan sanda a jihar Katsina sun kama wata matar aure mai suna Safiya Yakubu, kan zargin mallakar wata bindigar Travor-21.

Safiya, ta fada ma manema labarai a lokacin da aka gurfanar da ita, cewa makamin mallakar mijinta mai suna Yakubu ne a kauyen Runka, wanda yake amfani dashi wajen garkuwa da mutane.

Tace mijinta da wasu abokansa sun fada harkar ne na tsawon wani lokaci.

An kama wata matar aure da wani matashi da makamai a Katsina

An kama wata matar aure da wani matashi da makamai a Katsina
Source: Depositphotos

Kwamishinan yan sandan jihar, Sanusi Buba, yace an kama matar ne bayan wani mamaya da aka gudanar a ranar 11 ga watan Afrilu a kauyen Sabon Layin Sara, karamar hukumar Kafur da ke jihar wanda yayi sanadiyar arangama da wasu yan fashi da makami.

KU KARANTA KUMA: Kakakin majalisa: Kungiyar matasa sunce lallai Wase ne zabinsu

Hakazalika, wani mai suna Jibril Anas, wanda ya kammala jami’a a jihar, yace abokansa ne suka bashi shawarar siyan bindigar da aka kama shi dashi domin kare kansa.

Anas yace wani Usman dan asalin Benue ne ya hada shi da mai safarar makamin wanda ke zama a tsakanin Nasarawa da jihar Benue annan ya samo masa bindiga akan N7,000.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel