Ta bayyana: Yan sanda suka kaiwa masu garkuwa da mutane kudin fansa na - Wani Bature da aka sace

Ta bayyana: Yan sanda suka kaiwa masu garkuwa da mutane kudin fansa na - Wani Bature da aka sace

Wani dan kasar Canada mai suna, Kyliuk Morris, a ranar Talata ya bayyana cewa yan sanda a jihar Ogun suka taimaka wajen kaiwa masu garkuwa da mutane kudin fansan N2.5m kafin aka sakeshi.

Morris ya bayyana hakan ne a wani hira da yayi da jaridar Punch a Abeokuta, yadda wasu yan baranda sukayi garkuwa da shi a Fidiwo, karamar hukumar Obafemi-Owode na jihar Ogun.

Baturen ya ce yana tafiya garin Ibadan, jihar Oyo ne ranar 13 ga watan Maris, 2019 inda sukayi awon gaba da shi.

Ya laburta cewa kwananshi shida a dajin masu satar mutane, inda suka tilastashi cin Teba da ruwan sha mara kyau.

KU KARANTA: Sarakunan Zamfara sun saki jerin sunayen jama'ar gari da harin Soji ya kashe

Yace suna cikin mota kawai sai wasu yan bindiga suka budewa motar wuta. Hakan ya sa ya fada cikin rami. Yayinda matarsa tayi kokarin gudu, masu garkuwa da mutanen suka harbeta kuma suka shige dashi cikin daji.

Yace: "Na kwashe kwanaki shida a wajen masu garkuwa da mutane. Sun lallasa ni, yayinda uwargidata ke kokarin samun kudin fansa."

"Wani dan sanda ya amshi kudin fansan kuma ya kaiwa musu kafin aka sakeni. Kana dan sandan ya amshi 20,00 hannun uwargidata matsayin kudin mota."

"Ina son gwamnati ta san abinda ya faru da ni. Gwamnatin Najeriya na kukan cewa masu sanya hannun jari basu son shigowa kasar, musamman domin aikin noma, amma babu tsaro gaba daya."

Baturen yace sai da ya kira 'yar uwarshi dake Canada kafin ya iya biyan kudin fansan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel