Adeyemi ya nemi Kotu tace a sake zaben kujerar Sanatan Kogi ta Yamma

Adeyemi ya nemi Kotu tace a sake zaben kujerar Sanatan Kogi ta Yamma

A makon nan ne mu ka ji labari cewa Sanata Smart Adeyami wanda shi ne ‘Dan takarar jam’iyyar APC na kujerar Sanatan Kogi na shiyyar Yamma a zaben 2019 ya tafi kotun da ke sauraron karar zabe.

Smart Adeyemi ya maka kara a gaban kotun da ke karbar korafin zabe inda yake neman kotu ta soke zaben da ya ba Sanata Dino Melaye nasara. Adeyami yace yana da hujjojin da ke nuna cewa Dino Melaye bai ci zabe ba.

Sanata Adeyemi yake cewa takardun da ke hannun sa, sun tabbatar masa da cewa sakamakon da hukumar zabe ta bayyana inda ta sanar da cewa Dino Melaye na PDP ne ya lashe zaben Sanatan yankin, ba na gaskiya bane.

KU KARANTA: Rikici 4 da Dino Melaye ya shiga yana kan kujerar Sanata

Adeyemi ya nemi Kotu tace a sake zaben kujerar Sanatan Kogi ta Yamma

Adeyemi yana so Kotu ta soke zaben Dino Melaye
Source: Depositphotos

Tun farko Smart Adeyemi ya koka da canza wurin tattara kuri’un zabe da INEC tayi, inda yace kotu tace a Garin Kabba ya kamata a karbi sakamakon zaben yankin, amma hukumar ta sabawa wannan, ta tare a cikin Garin Lokoja.

Tsohon ‘Dan majalisar tarayyan yace don haka akwai bukatar a soke wannan zabe a sake gudanar da sabo domin an tafka magudi inda aka rika karawa PDP kuri’u, aka kuma yi coge wajen kada kuri’u a wasu akwatun zaben.

Adeyemi yana ikirarin cewa an karawa Dino Melaye kuri’u sama da 18, 000 na bogi a zaben, sannan kuma an yi watsi da na’urar tanrance masu kada kuri’a, inda aka rika barin jama’a su na dangwala kuri’a .

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel