Tinubu na mutunta ni a matsayin dan Buhari ta fuskacin siyasa – Bello

Tinubu na mutunta ni a matsayin dan Buhari ta fuskacin siyasa – Bello

Gwamna Yahaya Bello Bello na jihar Kogi a ranar Laraba, 17 ga watan Afrilu yace Asiwaju Bola Tinubu, babban jigon jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, ana mutunta shi sosai a matsayinsa na gwamnan jihar Kogi kuma dan Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta fuskacin siyasa.

Gwamnan yayi Magana ne ta bakin Kingsley Fanwo, Darakta Janar na labaran jihar Kogi a lokacin da ya bayyana a matsayin bako a shirin Channels YV ‘Politics Today’.

Da aka tambaye shi ko kudirin gwamna Bello na sake takara baya fuskantar barazana ta wajen Tinubu, Fanwo yace, “Gwamna Yahaya Bello na mutunta Asiwaju Bola Tinubu sosai.

Tinubu na mutunta ni a matsayin dan Buhari ta fuskacin siyasa – Bello

Tinubu na mutunta ni a matsayin dan Buhari ta fuskacin siyasa – Bello
Source: UGC

Ya ci gaba da cewa: "Hakazalika Asiwaju Tinubu ma na mututunta Gwamna Yahaya Bello a matsayinsa na gwamnan jihar Kogi kuma dan Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta fuskacin siyasa.”

KU KARANTA KUMA: Majalisar dattawa: Al’umman Borno sun jadadda goyon bayansu ga Ndume

A wani lamari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa, Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Laraba, ya yi bugun gaba na fifiko a siyasance ga babban abokin adawarsa, dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar adawa ta PDP, Atiku Abubakar.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, shugaban kasa Buhari ya misalta Atiku a matsayin dan siyasa da faduwar zabe ke bibiyar sa a duk inda ya sanya gaba. Ya ce faduwar zabe ga Atiku ta zamto tamkar jinin jikin sa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel