Majalisar dattawa: Al’umman Borno sun jadadda goyon bayansu ga Ndume

Majalisar dattawa: Al’umman Borno sun jadadda goyon bayansu ga Ndume

Wasu mutanen Borno masu kula sun jadadda goyon bayansu ga takarar Sanata Mohammed Ali Ndume na neman Shugabancin majalisar dattawa na gaba.

Mutanen sun nesanta kansu daga goyon bayan Sanata Ahmad Lawan da Gwamna Kashim Shettima yayi, cewa gwamnan ya fadi zuciyarsa ne amma ba zuciyar mafi akasarin mutanen Borno ba.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa sakataren kungiyar dattawan Brno, Dr. Bulama Mali Gubio ma a ranar Talata, 16 ga watan Afrilu ya karyata batun cewa kungiyar ta tsayar da Ndume a matsayin wanda take so ya zama Shugaban majalisar dattawa.

Majalisar dattawa: Al’umman Borno sun jadadda goyon bayansu ga Ndume

Majalisar dattawa: Al’umman Borno sun jadadda goyon bayansu ga Ndume
Source: Facebook

Sai dai, mambobin kungiyar mutanen Borno masu kula sun bayyana a jawabin daga kakakinsu, Uakubu Kwangyang Umar yayi cewa, "Abun mamaki ne cewa yayida jihar ke sauraron ganin gwamnan ya mara wa Sanata Ndume baya, sai gashi karara ya fito ya nuna cewa yana adawa da takararsa.”

A cewarsa, “daga cikin dalilan da yasa muke goyon bayan takarar Sanata Ndume shine gaskiyar cewa yana dauke da tunanin mutane a zuciyarsa, yana biyayya ga jam’iyya sannan ya samu dammar shugabancin mara sa ri njaye a majalisar wakilai tsakanin 2007-2011, sanata mai tarin kwarewa, shugaba masu rinjaye a majalisar dattawa 2015-2017, daraktan kungiyar kamfen din Shugaban kasa a arewa maso gabas 2019, da sauran muhimman abubuwa.”

KU KARANTA KUMA: Atiku bai taba samun nasarar zabe a kai na ba - Buhari

A baya Legit.ng ta rahoto cewa, Gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima, ya bayyana cewa al'ummar Borno za ta samu nasara kan Sanata Ali Ndume domin ya janyewa Sanata Ahmad Lawan, wanda jam'iyyar APC ta zaba matsayin dan takaranta na kujerar shugaban majalisar dattawa.

Shettima ya bayyana cewa a matsayinsu na masu biyayya ga jam'iyya, ya kamata su amince da zabin jam'iyyar kan ahmad Lawan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel